Ban Aikata Wani Laifi Ba, Jami’in REC Na INEC a Adamawa da Aka Dakatar Ya Yi Bayani Game da Zaben Jihar

Ban Aikata Wani Laifi Ba, Jami’in REC Na INEC a Adamawa da Aka Dakatar Ya Yi Bayani Game da Zaben Jihar

  • Kwamishinan zaben jihar Adamawa ya bayyana gaskiyar yadda zaben gwamnan jihar ya kasance
  • A cewarsa, wasu kwamishinonin INEC na kasa sun karbi cin hanci a hannun gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri
  • Wannan na fitowa ne daga inda Ari ke boye yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da neman inda yake

Najeriya - Dakataccen Kwamishinan Zabe (REC) a jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, ya ce ya ayyana 'yar takarar jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar ne domin ceto tsarin dimokuradiyya.

Ari ya ce ya yi aiki ne bisa ga ikon da dokar zabe ta ba shi a matsayinsa na babban jami’in tattara sakamakon zabe a jihar Adamawa, The Nation ta ruwaito.

Bayan nasa na kunshe ne a cikin wata wasika mai shafuka hudu da ya rubuta ya mika wa babban sifeton ‘yan sandan daga inda yake boye.

Kara karanta wannan

DSS Ta Tsare Hadimin Fintiri Da Magoya Bayan PDP Kan Kai Wa Ma'aikatan INEC Hari

Ari ya fadi dalilin da yasa yace Binani ce ta lashe zaben Adamawa
Jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Manyan jami'ai biyu sun karbi cin hanci daga Fintiri, inji Ari

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, ya zargi kwamishinonin INEC na kasa biyu da aka tura jihar domin sa ido kan zaben da aka karasa a ranar 15 ga watan Afrilu da karbar cin hanci daga gwamna Ahmadu Fintiri domin alanta shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan Afrilu 20, Ari da har yanzu ake takaddama kan aikinsa, ya kuma zargi kwamishinonin biyu da dauke nauyin da ya rataya a wuyansa na REC a jihar.

Abin da na aikata daidai ne

Ya musanta aikata ba daidai ba wajen ayyana Aishatu Dahiru (Binani) a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna inda ya ce abin da ya yi daidai yake da hakkin da dokar zabe ta dora masa a matsayin kwamishinan zabe na jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun tarayya ta yanke hukunci kan karar da Binani ta shigar game da zaben Adamawa

Ya ce a matsayinsa na Babban Jami’in tattara zaben jihar, ya lura cewa sakamakon da aka dora a tashar IREV ba shi ne ya sa hannu akai ba, don haka ba sahihi bane, rahoton Daily Trust.

Har yanzu dai Ari bai bayyana ba, kuma ana ci gaba da neman inda yake don yi masa titsiye game da ayyukansa na zaben gwamnan Adamawa.

A baya, shugaba Buhari ya ce a gaggauta kamo Hudu Ari tare da bincikarsa da kuma hukunta shi idan ya aikata laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel