An Gama da Binani, Kotun Abuja Ta Kori Karar da Aka Shigar Na Kalubalantar Sakamakon Zabe

An Gama da Binani, Kotun Abuja Ta Kori Karar da Aka Shigar Na Kalubalantar Sakamakon Zabe

  • Aisha Binani ta gamu da rashin nasara a gaban kotu bayan da aka yi watsi da karar da ta shigar kan sakamakon zaben Adamawa
  • Binani ya nemi a dawo da sanarwar da Hudu Ari na cewa ita ta lashe zaben gwamna, lamarin da bai dauki hankalin alkali ba
  • A tun farko an samu tsaiko a yadda zaben jihar Adamawa ya kasance, inda aka yi tashin hankali bayan sanar da sakamako

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da karar da ‘yar takarar gwamnan APC, Aisha Dahiru Binani ta shigar game da sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa.

A baya, ta maka hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a gaban kotu tare da bayyana bukatar a dawo da ayyana ta a matsayin sabuwar gwamnan Adamawa da kwamishinan zabe ya sanar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Sa Labule da Shugaban APC Na Kasa da Wasu Jiga-Jigai, Bayanai Sun Fito

A lokacin da ake ambatan karar a ranar Laraba 26 Afirilu, 2023, lauyan Binani ya sanar da mai shari’a cewa, sun janye daga karar, inda suka nemi a cire takardar a gaban kotu.

Yadda aka haramtawa Binani mulkin Adamawa
Jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Sai dai, a hukuncin da mai shari’a Inyang Ekwo ya yanke, ya zabi ya kori karar gaba daya a madadin barin Binani ta janye, The Nation ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda zaben Adamawa ya kasance

Idan baku manta ba, an karasa zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu don cike gurbin zaben da aka fara aka kuma dakatar a watan Maris din da ya gabata.

A tun farko, kwamishinan zaben Adamawa, Hudu Ari ya yi riga malam masallaci, inda ya sanar da sakamakon zaben ba tare da jiran cikakkensa ba daga bangarori daban-daban na jihar.

Wannan ya haifar da cece-kuce da tashin hankali a jihar, har ta kai rikici ya barke bayan alanta Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben jihar.

Kara karanta wannan

Zaben Adamawa: Zababben Shugaban kasa, Tinubu ya yi kira ga ‘Yan Sanda da Binani

Daga baya an dakatar da tattara sakamakon zaben tare da umartar Hudu ya gaggauta zuwa Abuja domin gano kan zaren batun, TheCable ta tattaro.

Daga baya an sanar da sakamakon zabe na gaskiya, inda aka ce Ahmadu Fintiri na PDP ne ya lashe zaben da aka gudanar da wasu adadi na kuri’u.

Za a binciki Hudu Ari bisa laifinsa

A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a kama tare da bincikar Hudu Ari bisa zarginsa da tada hankali a jihar ta Adamawa.

Buhari ya ba da umarnin kama Hudu ne ga hukumar ‘yan sanda, DSS da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki kan lamarin da ya jawo cece-kuce.

Hakazalika, ya ce a bincike shi tare da gano tushen lamarin da kuma hukunta shi idan ya saba doka ko aka gano da saninsa ya aikata irin wannan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel