Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sako Kwamishiniyar Hukumar NPC a Jihar Rivers

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sako Kwamishiniyar Hukumar NPC a Jihar Rivers

  • Bayan kwashe kwanaki, ƴan bindiga sun sako kwamishiniyar hukumar ƙidaya ta ƙasa da suka sace a jihar Rivers
  • An dai yi awon gaba da Mrs Gloria Izonfuo ne a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da ta ke dawowa daga tafiya
  • Rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta tabbatar da sakin Mrs Gloria, sai dai ba ta bayyana ko an biya kuɗin fansa ba

Jihar Rivers - Kwamishiniyar hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) a jihar Bayelsa, da aka sace a jihar Rivers, Mrs Gloria Izonfuo ta shaƙi iskar ƴanci, rahoton Punch ya tabbatar.

Mrs Gloria ta shaƙi iskar ƴanci ne bayan ta kwashe kwana biyar a hannun ƴam bindigan da suka sace ta yankin Ogbakiri na titin hanyar East-West a jihar Rivers.

An sako kwamishiniyar NPC a Rivers
Kwamishiniyar NPC Mrs Gloria da aka sace a jihar.Rivers Hoto: Punch.com da Kanyinews.com
Asali: UGC

Mrs Izonfuo, wacce tsohuwar shugabar ma'aikatan jihar Bayelsa ce, an yi awon gaba da ita ne yayin da ta ke dawowa daga wata tafiya da ta je a garin Brass, na jihar Bayelsa a ranar Lahadin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An Samu Wata Fashewa A Babban Birnin Jihar Arewa, Mutane da Yawa Sun Mutu

Ƴan bindigan sun tafi da ita ne tare da direban ta da kuma ƴar aikin ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ƴan sanda sun tabbatar da an sako ta

The Eagle Online tace kakakin rundunar ƴan sandan jihar Rivers, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da cewa an sako kwamishiniyar a safiyar ranar Juma'a.

A kalamanta:

"Eh tabbas an sako ta yau (Juma'a) da safe. Ana cigaba da gudanar da bincike domin ganin an kamo waɗanda suka yi garkuwa da ita domin su fuskanci hukunci."

Ko da aka tambaye ta shin ko tare da direba da kuma ƴar aikin Mrs Gloria aka sako, sai kakakin ta amsa a gaggauce da cewa:

"Toh zan tuntuɓe ku kan hakan"

Sai dai, babu tabbacin cewa ko an biya kuɗin fansa kafin a sako kwamishiniyar.

Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Hakimi a Jihar Zamfara

Kara karanta wannan

Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa

A wani rahoton na daban kuma, wasu azzaluman ƴan bindiga sun sace wani basarake mai sarautar hakimi a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan dai sun kutse har cikin gida sannan suka yi awon gaba da hakimin Kasuwar Daji, wacce ke a ƙaramar hukumar Kauran Namoda ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel