Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Hakimi a Jihar Zamfara

Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Hakimi a Jihar Zamfara

  • Yan bindiga sun sace hakimin kasuwar Daji, ƙaramar hukumar Kauram Namoda a jihar Zamfara, Ibrahim Sarkin Fada
  • Mazauna garin sun bayyana cewa maharan ba su taba kowa ba, da zuwa suka zarce gidan Basaraken suka tafi da shi
  • Har yanzun hukumar yan sanda ba ta ce komai game da lamarin ba, kakakin yan sanda bai ɗaga kira ko turo amsar sakonni ba

Zamfara - 'Yan bindigan jeji sun yi garkuwa da Sarkin fadar Kasuwar Daji, da ke yankin ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar Zamfara, Ibrahim Sarkin Fada.

Jaridar Punch ta tattaro cewa yam fashin jejin sun kutsa har cikin gidan Basaraken kana suka yi awon gaba da shi a farkon awannin wayewar garin Alhamis.

Ibrahim Sarkin Fada.
Miyagun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Hakimi a Jihar Zamfara Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Wani haifaffen yankin, Malam Audu Mohammed, ya tabbatar da cewa yan bindigan da adadi mai yawa sun kutsa kai cikin garin Kaauwar Daji, suka tafi kai tsaye zuwa gidan Basaraken.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Yan Farin Hula 15 Da Sojoji 2

Ya ce daga zuwa suka kutsa cikin gidan suka ɗauki Ibrahim Sarkin Fada, suka tasa shi zuwa maɓoyarsu da babu wanda ya sani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Audu ya ce yan fashin jejin sun buɗe wuta domin tsoratar da mutanen garin, waɗanda suka yi yunkurin ceton Sarkinsu.

A kalamansa ya ce:

"Ina cikin gida lokacin da na fara jiyo ƙarar harbe-harben bindiga da misalin ƙarfe 2:30 zuwa karfe 3:00 na dare wayewar garin Alhamis."
"Daga baya wani abokina ya kira ni a waya da misalin karfe 4:00 na wannan daren, a wurinsa na samu labarin an sace Dagacin garin mu."

Premium Times ta rahoto cewa Kasuwar Daji na ɗay daga cikin garuruwa masu zaman lafiya a yankin ƙauram Namoda.

Sai dai sace Hakimi ya jefa mazauna garin da sauram yankunan da ake zaman lafiya cikin ruɗani da fargaba a cewar Ubaidullah Kaura, wani mazaunin Ƙauran Namoda.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Masu Garkuwa Da Mutane Sun Bi Dare Sun Kwamushe Bayin Allah a Arewacin Najeriya

Har yanzun rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ba ta ce komai ba game da sabon harin ba kuma duk kiran da aka wa kakakin rundunar, Muhammed Shehu, da saƙonnin da aka tura masa bai amsa ko ɗaya ba.

Shugaba Buhari Ya Isa Wurin Faretin Sojoji Sanye Da Kakin Soji

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari Ya Dira Wurin Faretin Sojojin Najeriya Sanye Da Kakin Soji

Shugaban ƙasa ya isa wurin da karfe 10:18 na safiyar ranar Alhamis tare da rakiyar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

Shugabannin sojojin ƙasa na ruwa da sama duk halarci wurin tare da sufetan yan sanda na ƙasa, Usman Baba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel