Yan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah 15 Da Sojoji 2 a Jihar Benue

Yan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah 15 Da Sojoji 2 a Jihar Benue

  • Yan bindiga sun kai mummunan hari kan al'ummar wasu garuruwa uku a jihar Benue a ranar Talata
  • Maharan sun sheke yan farin hula 15 da wasu dakarun sojoji guda biyu a kokarinsu na dakile harin
  • Da take martani, rundunar yan sandan jihar Benue ta ce bata da masaniya a kan harin

Benue - Rahotanni sun kawo cewa sojoji biyu da yan farin hula 15 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da yan bindiga suka kai kan garuruwa uku a karamar hukumar Apa ta jihar Benue.

Mazauna yankin sun bayyana cewa an kai hare-haren ne a lokaci guda da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Talata, a garuruwan Opaha, Odogbo da Edikwu a karamar hukumar Apa, Daily Trust ta rahoto.

Wani mazaunin yankin da aka ambata da suna Kole, ya ce gawarwakin mutum 17 ciki harda sojoji biyu ne aka gano daga wasu jeji da ke kusa a safiyar ranar Laraba bayan jami'an tsaro sun kakkabe yankin.

Kara karanta wannan

Mummunan karshe: Sojoji sun aika 'yan bindiga 5 madakata, sun kwato shanu da makamai

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Yan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah 15 Da Sojoji 2 a Jihar Benue Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewa daya daga cikin sojojin da suka mutu ya kasance kwamandan sashin da ya yi gaba da gaba da maharan ne a kokarinsu na dakile harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kungiyar ci gaban Apa, Baris Eche Akpoko ya tabbatar da cewar an kai wani hari kan garin a daren ranar Talata, rahoton TVC News.

Akpoko ya ce gawarwakin mutane 10 ciki harda na sojoji biyu aka gano amma cewa har zuwa karfe 10:30 na safe bai samu karin bayani kan lamarin ba.

Kwamishinan kudi na jihar, David Olofu, wanda ya fito daga yankin Opaha,daya daga cikin kauyukan da abun ya shafa, ya fada ma manema labarai a Makurdi cewa gawarwaki mazauna kauyen 15 da sojoji biyu aka gano a safiyar Laraba.

Olofu ya ce yana hanyarsa ta zuwa kauyen don duba lamarin a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Mutum 5 Sun Rasu A Hadarin Jirgin Ruwa A Kano, An Ceto Wasu Shida Da Ransu

Kakakin OPWS, Flight Lieutenant DO Oquah, ya ce baya gari kuma ba zai iya magana kan lamarin ba.

Rundunar yan sanda ta yi martani

A halin da take ciki, kakakin rundunar yan sandan Benue, SP Catherine Anene, ta sanar da Daily Trust cewa har yanzu bata da masani kan lamarin.

A wani labari na daban, dakarun rundunar sojojin Najeriya ta halaka mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram masu yawan gaske a wani hari da suka kai sansaninsu a dajin Sambisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel