Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar Hujjar da ke Fallasa 'Magudin' Bola Tinubu

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar Hujjar da ke Fallasa 'Magudin' Bola Tinubu

  • ‘Dan takaran LP a zaben bana, Peter Obi ya zargi INEC da yin magudi saboda APC ta zarce a mulki
  • Peter Obi ya ce hukumar INEC tayi haka ne ta hanyar kirkiro matsalolin karya a kan shafin iRev
  • Lauyan da ya shigar da kara a madadin Jam’iyyar LP ya ce bayanai sun tabbatar da an yi masu coge

Abuja - Peter Obi wanda ya shiga zaben 2023 a matsayin ‘dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar LP, ya na zargin magudi ya ba Bola Tinubu nasara.

A ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto Mista Peter Obi yana ikirarin hukumar INEC ta murde zaben shugaban kasa ta yadda jam’iyyar APC tayi galaba.

Wannan yana cikin bayanin ‘dan takaran da jam’iyyar adawar a kotun da ke sauraron korafin zabe.

Burin LP da Obi shi ne a rusa nasarar da INEC ta Bola Tinubu a zaben da ya gabata, suke cewa wasa da hankalin mutane aka yi saboda ayi aika-aika.

Kara karanta wannan

Zaben Majalisa: An Bar APC Da Ciwon Kai, Mutanen Arewa Maso Yamma Sun Huro Wuta

Akwai alamar tambaya?

Lauyan da ya tsaya masu, Levy Uzoukwu (SAN) ya ce babu wani kwakkwaran dalilin da zai hana hukumar zabe daura sakamako a kan shafin yanar gizo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Lauyan, wajibi ne ayi amfani da IReV, a rika wallafa kuri’un da mutane suka kada, amma a karshe ba ayi hakan ba saboda an shirya rashin gaskiya.

Peter Obi
Mr. Peter Obi wajen kamfe Hoto; Getty Images
Asali: Getty Images

Matsalar bogi ce - Lauya

An rahoto Levy Uzoukwu yana mai fadawa kotun sauraron karar zaben da ke zama a garin Abuja cewa da gan-gan kurum aka kirkiri matsalar HTTP 500.

Wadanda suka tsayawa LP da ‘dan takaranta a kotu sun zargi hukumar zabe na kasa da gaggawar sanar da Tinubu a matsayin zababben shugaban Najeriya.

Kamar yadda jam’iyyar take fada, ‘dan takaran na APC bai samu akasarin kuri’un da aka kada ba, domin ana zargin an rage kuri’un Obi a zaben da aka yi.

Kara karanta wannan

Babu Murdiya, Babu Magudi – Minista Ya Ambaci Silar Nasar Tinubu a Zaben 2023

Yadda za a gane hakan, Uzoukwu ya ce a duba bayanan da ke kan na’urar hukumar zabe.

Binciken kwararru da aka gudanar a kan cogen da aka yi wa LP a zaben shugaban kasar yana cikin hujjojin da lauyan ya gabatar da nufin gamsar da Alkalai.

An yi magudi a jihohi 2 - Peter Obi

Ba wannan ne karon farko ba, a baya an ji labari Peter Obi ya na da’awar cewa jam’iyyarsa ta LP ce ta yi nasara a zaben 2023, amma aka murde masa.

‘Dan takaran yana so a soke wasu kuri’un da INEC ta ba Bola Tinubu, a cewarsa APC tayi magudi a Ribas, sannan LP ta fi kowa yawan kuri’u a Benuwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng