Dauda na Shirin a Rantsar da Shi, Matawalle Ya Sheka Kotu Kan Zaben Gwamnan Zamfara

Dauda na Shirin a Rantsar da Shi, Matawalle Ya Sheka Kotu Kan Zaben Gwamnan Zamfara

  • Bello Muhammad Matawalle bai yarda Jam’iyyar PDP ta doke shi a zaben Gwamnan Zamfara ba
  • Mai ba Gwamnan shawara, Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi ya ce tun tuni sun kai kararsu a kotun zabe
  • A cewar Suleiman Shinkafi, Dauda Lawal Dare bai doke Gwamna Matawalle a zaben bana da aka yi ba

Zamfara - Bello Muhammad Matawalle ya ce zai yi nasara a kotun sauraron karar zabe, ya cigaba da mulki a matsayin Gwamnan jihar Zamfara.

Labari ya zo daga Daily Trust cBello Muhammad Matawalle bai gamsu da sakamakon zaben jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris ba.

Mai girma Gwamna Bello Muhammad Matawalle wanda ya nemi tazarce a jam’iyyar APC mai-ci ya sha kashi a hannun Dauda Lawal Dare na PDP.

Gwamnan ya kalubalanci nasarar da hukumar INEC ta ba ‘dan takaran jam’iyyar adawa ta PDP, ya tabbatar da tuni ya kai maganar gaban kotu.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar ‘Hujjar’ da ke Nuna Magudin Bola Tinubu

Gwamna ya taya Dauda murna?

Wani hadimin Gwamnan Zamfara, Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi ya yi karin haske cewa mai gidansa bai taya Dauda Lawal murnar cin zabe ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akasin abin da ake yadawa, rahoton ya ce Gwamnan yana hangen nasara a kotun korafin zabe.

Gwamnan Zamfara
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi yake cewa zabukan da aka yi da sakamakon da aka sanar a watan Maris tamkar fashi da makami ne da rana tsaka.

Leadership ta ce Mai ba Gwamnan shawara ya ce ana kalubalantar wannan nasara da ake ikirarin PDP ta samu, tare da kira ga APC ta binciki zaben.

Jawabin Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi

“Babu ta yadda mutanen kirkin Zamfara za su ki zaben Gwamna Bello Matawalle ganin irin aikin da ya yi a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun tarayya ta yanke hukunci kan karar da Binani ta shigar game da zaben Adamawa

Saboda haka ba za muyi sake wajen ganin mun samu nasarar karbe kujerarmu a kotu ba.
Mu na kotun karbar karar zabe domin kalubalantar ayyana Dauda Lawal na PDP a matsayin zababben Gwamna.
Ba za mu yarda da wannan ba domin ba gaskiya ba ne a ce (Dauda Lawal) ya lashe zaben.”

- Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi

Tinubu ya ci zabe ko bai ci ba?

A jiya aka ji labari Lauyan jam’iyyar LP a kotun zaben shugaban kasa, ya ce ‘dan takaran su ne ya yi galaba, amma Jam’iyyar APC ta hada-kai da INEC.

‘Dan takaran Shugaban kasar watau Peter Obi ya ce bayanan da ke fitowa daga Hukumar INEC sun tona asirin magudin da aka yi saboda Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel