Shugaba Buhari Ya Yi Umrah Cike Da Tsaro a Garin Makkah

Shugaba Buhari Ya Yi Umrah Cike Da Tsaro a Garin Makkah

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Umrah a garin Makkah, kasar Saudiyya
  • Da isarsa masallacin cikin tsauraran matakan tsaro, Buhari ya samu tarba daga tawagar fadar shugaban kasa kan harkokin masallacin harami
  • Tare da shi akwai ministan sadarwa, Sheikh Ali Isa Pantami da sauran jami'an gwamnatin Najeriya

Saudiyya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi aikin Umrah cike da matakan tsaro, bayan ya isa masallacin Harami da ke garin Makkah, kasar Saudiyya a ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu.

A cewar wata sanarwa da babban mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar, shugaban kasar ya samu tarba daga jami'an Saudiyya da na Najeriya.

Shugaba Muhammadu Buhari yana Umrah
Shugaba Buhari Ya Yi Umrah Cike Da Tsaro a Garin Makkah Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Daga cikin wadanda suka tarbe shi harda wata tawagar fadar shugaban kasa kan harkokin Masallacin harami da ma'aikatan ofishin Jakadancin Najeriya, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Isa Birnin Madina, Ya Ziyarci Masallacin Annabi

Da farko dai shugaban kasar ya fara zuwa birnin Madina inda ya yi sallah a masallacin Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, shugaban kasar ya ziyarci kabarin Annabi da manyan sahabbansa biyu.

Buhari dai ya isa kasar Saudiyya ne a ranar Talata inda zai kai ziyarar aiki na tsawon kwanaki takwas.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin zumunta na zamani, Bashir Ahmad ya wallafa hotunan shugaban kasar tare da ministan sadarwa, Sheikh Ali Isa Pantami da sauransu a masallacin Harami

Ga wallafar tasa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Clericcoder ya ce:

"Masahallahu, Allah a cikin rahamarsa ya karbi ibadah."

@attajiree_atiku ya ce:

" Allah sarki umara sa kenan ta karshe a matsayin sa na shugaban kasar Nigeria in ya koma sai dai ace tsohon shugaban kasar Nigeria."

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Bayyana Koma Bayan da Rashin Lafiyar Shugaba Buhari Ta Jawo a Najeriya

@AminuIn52962630 ya ce:

"Taron munafukai adakin Allah munaroqan Allah yaimana sakaiya tsakaninmu dasu."

@IbrahimYusufah6 ya ce:

"Allah yakarbi ibadah mlm Ana uhibuka fillah."

@talk2srm ya ce:

"Anje Ta Ban Kwana Allah Yasa Anyi Karbar Biya."

@SadiqUsaku ya ce:

"Allah yakarbq ibadunmu."

@GMatxai ya ce:

"Allahu Akbar!!! Allah yasa muna da rabbon zuwa...."

Tinubu ya fasa zuwa Landan da Saudiyya don yi Umrah daga Paris

A wani labari na daban, mun kawo cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zababben shugaban kasar Najeriya ya fasa zarcewa birnin Landan da kasar Saudiyya don yin aikin Umarah daga birnin Paris.

An tattaro cewa hakan baya rasa nasaba da wutar rikicin da ke shirin kunno kai a jam'iyyar APC saboda fafutukar zababbun yan majalisar tarayya da ke neman shugabancin majalisar ta 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel