Abba Gida-Gida Ce Duk Masu Gini Kan Filin Gwamnati a Kano Su Gaggauta Dakatar da Aikin

Abba Gida-Gida Ce Duk Masu Gini Kan Filin Gwamnati a Kano Su Gaggauta Dakatar da Aikin

  • Zabebben gwamnan Kano ya shawarci wadanda suka sayi filayen gwamnati a jihar da su dakata da yin gini a kai tukuna
  • Gwamnan ya ce, yana da kudurin dawo da martabar birnin Kano, don haka akwai shirin da yake dashi a kasa game da filayen
  • A baya, Abba Gida-Gida ya sha sukar gwamnatin Ganduje game da batun siyar da filayen gwamnati ag daidaikun jama’a a jihar

Abba Kabir Yusuf, sabon gwamnan jihar Kano ya tura sakon gargadi da shawari mai zafi ga masu gine-gine a filayen gwamnati a duk inda suke a jihar.

A cewarsa, duk wanda ya san yana gini a kan filin gwamnati to ya dakata nan take har sai gwamnati ta sake yin magana kan lamarin.

Abba Gida-Gida ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya fitar a ranar Juma’a 31 ga watan Maris a shafinsa na sada zumunta; Facebook.

Kara karanta wannan

To fah: A kama Atiku da Peter Obi kawai, cewar jigon APC bisa muhimmin dalili

Abba Gida-gida ya tura sako ga wadanda suka sayi filin gwamnati a Kano
Abba Kabir Yusuf, zababben gwamnan Kano | Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Shawarin Abba Gida-Gida ga jama’ar Kano

Sakon da ya wallafa ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Kamar yadda muka kuduri aniyar dawo da tsarin birnin Kano; Ina shawartar Jama'a da su daina duk wani aikin gine-gine na filayen gwamnati a ciki da wajen makarantu, wuraren addini da na al'adu, da dukkan asibitoci, da makabarta, da kuma gefen katangar birnin jihar Kano.”

A bangare guda, jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, mai magana da yawun zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar da sanarwa mai bayyana bayani irin wannan.

A cewar Bature, ana shawartar duk wasu da ke aikin rushewa ko gini a filayen na gwamnati to su tabbatar da sun dakata a halin da ake ciki.

Abba Gida-Gida dai ya sha bayyana sukar gwamnatin Ganduje da ke siyar da filayen jihar ta Kano ga daidaikun mutane ‘yan kasuwa a bangarori daban-daban.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan 2023: Taya Murnar Nasir Yusuf Gawuna Ga Abba Kabir Yusuf Gida-Gida

An ba Abba Gida-Gida takardar shaidar lashe zabe

A wani labarin, kunji yadda aka ba Abba Gida-Gida takardar shaidar lashe zaben gwamna a jihar ta Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

A hotunan da aka yada, an ga lokacin da gwamnan ya karbi takardar tare da dandazon magoya bayansa da jam’iyyar NNPP ta su Kwankwaso.

A zaben gwamnan da ya gabata, Abba Kabir ne ya lashe zabe, inda ya lallasa Gawuna na jam’iyyar APC ta su gwamna mai barin gadi; Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel