Ashsha: Yadda Aka Babbake Wani Matashi Kan Zargin Satar Wayar Android

Ashsha: Yadda Aka Babbake Wani Matashi Kan Zargin Satar Wayar Android

  • Wani ɓarawo ya gamu da ajalin sa bayan wasu matasa sun cinna masa wuta a Cross River
  • Ana zargin matashin mai ƙananan shekaru da laifin satar wayar salula ta Android ya arce da ita
  • Jami'an ƴan sanda sun yi tofin Allah tsine kan yadda matasan suka ɗauki doka a hannunsu wajen hukunta ɓarawon

Jihar Cross River- Wasu matasa sun yi wa wani matashi mai shekara 22, taron dangi inda suka cinna masa wuta bisa zargin satar wayar Android a unguwar Atimbo, cikin ƙaramar hukumar Calabar Municipal a jihar Cross River.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa wani ganau ba jiyau wanda ya bayyana yadda lamarin ya auku, ya ce matashin mai suna Eyo riƙaƙƙen ɓarawo ne a yankin sannan an sha jan kunnen sa kan ya daina sata.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ministan Buhari Kan Abu 1? Gaskiya Ta Bayyana

An babbake barawon wayar Android
An Babbake Wani Matashi Kan Zargin Satar Wayar Android Hoto: iStock.com
Asali: UGC

Ganau ɗin wanda ya nemi da a sakaya sunan sa, ya ce Eyo ya tafka satar ne a ranar Asabar, inda yayi ɓata dabo ba a sake jin ɗuriyarsa ba har sai ranar Lahadi.

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Na san Eyo tun muna makarantar sakandire, ya saba da sata, akwai lokacin da ya sace kusan rabin kuɗin makarantar ƴan ajin mu."
"Yayin da muke ƙara girma sai Eyo ya cigaba da zama riƙaƙƙen ɓarawo, satar sa ta ƙara munana, an sha kama shi sau da dama, wannan ba shi bane karon farko da aka taɓa yi masa taron dangi ba, yau dai kawai ya haɗu da ajalin sa."
"Sun fara dukan shi da adda kafin su cinna masa wuta. Abin mamaki shine ba sayar Android kawai yayi ba."

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Matasa Sama da 80 Yau Jumu'a a Jihar Arewa

Kakakin hukumuar ƴan sandan jihar, Irene Ugbo, ta tabbatar da aukuwar lamarin sannan tayi Allah wadai da abinda matasan suka aikata.

A yayin da take nuni da cewa ya saɓa doka mutane su ɗauki hukunci a hannun su, ta ce abinda yakamata ayi shine a miƙa wanda ake zargin zuwa ofishin ƴan sandan da ke a unguwar, cewar rahoton Vanguard

"Halaka shi ta wannan mummunar hanyar, ba wai kawai jahilci bane, ya saɓawa doka sannan bai dace ba." A cewar ta

Yan Sanda Sun Sheke ’Yan Bindiga 2 a Zamfara

A wani labarin na daban, kun ji yadda ƴan sanda suka yi ajalin wasu tsagerun ƴan bindiga biyu a jihar Zamfara.

Ƴan sandan sun kuma nasarar raunata da damaa daga cikin ƴan bindigan sa suka hana al'ummar jihar sakewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel