Yan Bindiga Sun Sace Matasa Maza da Mata 80 a Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Sace Matasa Maza da Mata 80 a Jihar Zamfara

  • 'Yan ta'adda sun yi awon gaba da matasa maza da mata aƙalla 80 a kauyen Wanzamai, jihar Zamfara
  • Mazauna kauyen sun ce matasan sun shiga jeji ne domin ɗebo itatuwan girki amma suka tsinci kansu a hannun maharan
  • Lamarin wanda ya faru ranar Jumu'a da misalin karfe 8:00 na safe, ya shafi kusan kowa a kauyen

Zamfara - Matasan da basu gaza 80 ba da suka shiga cikin Jeji ɗebo Itatuwan girki sun shiga hannun 'yan ta'adda da ake zaton sun yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Vanguard ta rahoto cewa lamarin, wanda ya auku a ƙauyen Wanzamai da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Jumu'an nan ya jefa mutanen ƙauyen cikin firgici da tashin hankali.

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Sace Matasa Maza da Mata 80 a Jihar Zamfara Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Duk wani yunkurin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar ko gwamnatin Zamfara ya ci tura har zuwa yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Duk Da Shugaba Buhari Ya Sako Kudi, ASUU Tace Akwai Sauran Rina a Kaba

Amma iyayen da aka yi garkuwa da 'ya'yansu sun shaida wa BBC Hausa a wata hira cewa yan ta'addan sun sace matasan yaransu maza da mata yayin da suka je ɗebo Itace a Jeji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wani mahaifi, "Lamarin ya shafi kowa a kauyen, ko dai ɗanka ko ɗiyarka na cikin wadanda ke tsare a hannun yan ta'adda, ko kuma ya'yan yan uwanka. Ni kaina sun tafi da ɗana da Babur ɗina."

Wata mata a ƙauyen Wanzamai ta ce ɗiyarta yar shekara 15 a duniya na cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.

"Mun shiga damuwa saboda bamu san halin da 'ya'yanmu ke ciki ba a hannun yan bindiga," inji ta.

Har kawo yanzun da muka kawo muku wannan labarin yan ta'addan ba su tuntubi kowa game neman kuɗin fansa ba, kamar yadda DailyTrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwantan Bauna, Sun Kashe Da Dama

Bayanai sun nuna cewa 'yan ta'adda sun kai hari a baya farkon watan Ramadan kan mazauna kauyen Wanzamai amma dabbobi kaɗai suka sata suka yi gaba.

An kashe yan sanda uku a Edo

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Bauna, Sun Kashe Yan Sanda Uku a Jihar Edo

An ce yan sandan na kan hanyar zuwa inda suka saba kafa shinge, ba zato ba tsammani yan bindigan suka buɗe musu wuta a kusa da wata kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel