Ministan Kasahen Waje Ya Musanta Jita-Jitar da Ake Yadawa a Kansa

Ministan Kasahen Waje Ya Musanta Jita-Jitar da Ake Yadawa a Kansa

  • Ministan kasashen waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa jam'iyyarsa APC ta dakatar da shi
  • A wata sanarwa da ma'aikatar waje ta fitar ranar Asabar, ta ce zargin da ke kunshe a cikin rahoton ba gaskiya bane
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kace-nace kan sautin muryar Peter Obi da wani malin majami'a

Ministan harkokin kasahen waje, Geoffrey Onyeama, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa jam'iyyar APC ta dakatar da shi kan zargin ƙin bin umarninta.

Ministan ya ayyana jita-jitar da ƙarya tsagwaronta, wacce ake zargin APC ta dakatar da shi saboda ya ƙi aminta da kudirinta na ɓata sunan ɗan takarar Labour Party, Peter Obi.

Ministan harkokin kasahen waje, Geoffrey Onyeama.
Ministan kula da harkokin kasashen waje na Najeriya, H.E Geoffrey Onyeama Hoto: Geoffrey Onyeama
Asali: Depositphotos

Punch ta rahoto cewa raɗe-raɗin wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa Onyeama zai aiwatar da wannan aiki da aka sanya shi a ƙasar Amurka.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Sace Matasa Sama da 80 Yau Jumu'a a Jihar Arewa

Menene gaskiya rahoton?

Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar harkokin kasashen waje, Misis Francisca Omayuli, ta fitar ranar Asabar 8 ga watan Afrilu, ta roki ɗaukacin 'yan Najeriya su yi watsi da jita-jitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton Dailypost, Sanarwan ta ce:

"An jawo hankalin ma'aikatar harkokin kasashen waje kan wani labari da ke yawo a Sohiyal Midiya cewa jam'iyyar the All Progressives Congress (APC) ta dakatad da ministan kasashen waje, H.E. Geoffrey Onyeama."
"An yi zargin cewa, 'Jam'iyya ta tura shi ya ɓata sunan Peter Obi a ƙasar Amurka amma ya ce ba zai yi ba'. Ministan harkokin kasashen na tabbatar muku da cewa babu ƙanshin gaskiya a labarin kuma zargi ne gurbatacce."
"Sakamakon haka muna kira ga ɗaukacin al'umma kar su yarda da labarin, su yi fatali da shi domin ƙanzon kurege ne."

Kara karanta wannan

Zababben Gwamnan APC Ya yi Kus-Kus Da Shugaba Buhari, Ya Ce Jiharsa Na Neman Dauki

NAHCON Ta Sanar da Kuɗin Kujerar Sauke Farali, Ta Raba Su Zuwa Kaso 8

A wani labarin kuma Daga Karshe An Bayyana Kuɗin Zuwa Hajjin Bana 2023, Ya Kasu Zuwa Gida 8

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar jin daɗin alhazai ta tarayyan Najeriya (NAHCON) ta sanar da miliyan N2.8m a matsayin kuɗin kujerar Hajjin 2023.

Sai dai shugaban NAHCON ya bayyana cewa kuɗin kujerar ya rabu kashi-kashi har kashi 8 ya danganta da yankin da maniyyaci ya fito a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel