An Kama Wani Matashin da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje a Harin ’Yan ISWAP

An Kama Wani Matashin da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje a Harin ’Yan ISWAP

  • ‘Yan sanda sun kame wani matashi da ake zargin ya tsere daga gidan yarin Kuje da aka farmaka a shekarar da ta gabata
  • An kuma kama shi tare da wani mutum da ake zargin sun yi kwacen babur a wani yankin jihar da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya
  • Ba wannan ne karon farko da ake kama wadanda suka tsere daga gidan yarin da aka farmaka a shekarar da ta gabaa ba

Jihar Nasarawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta yi nasarar kame wani fursunan da ya tsere da gidan yarin Kuje a harin ‘yan ta’adda na shekarar da gabata a Abuja, Daily Post ta tattaro.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa, wanda aka kamen matashi ne mai shekaru 24 mai suna Salisu Buhari dan asalin jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

An samu tangarda: Saurayi ya fusata, ya kone gidan su tsohuwar budurwarsa kurmus

Hakazalika, an kama wani tare da Salisu a wani aikin ‘yan sanda a karamar hukumar Nasarawa ta jihar mai suna Zubairu Ali mai shekaru 27.

An kama fursunan da ya tsere a Kuje a jihar Nasarawa
Jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Abuja | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Meye laifin da suka aikata?

Dukkansu biyun an kama su ne a ranar Alhamis din da ta gabata bisa zarginsu da sace babur, kamar yadda rahoton Channels Tv ya bayyana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar sanarwar:

“Binciken farko ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi kwancen babur tare da sace shi a karamar hukumar Nasarawa da kewayenta.
“Bayan titsiye su, Salisu Buhari ya amsa laifinsa na tserewa daga magarkamar Kuje a lokacin da aka farmaki gidan yarin a bara, inda ya hade da abokinsa, kuma suka ci gaba da aikata barnarsu.”

DSP Nansel ya ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Maiyaki Baba ya umarci a mayar da kundin matasan biyu zuwa sashen binciken manyan laifuka da ke Lafia don yin cikakken bincike.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Sansanin Yan Gudun Hijira a Arewa, Sun Kashe Mutane Sama da 40

Fursunoni sama da 300 ne suka tsere a harin gidan yarin Kuje

A tun farko, kunji yadda rahotanni suka bayyana adadin wadanda suka tsere a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai farmaki a gidan yarin Kuje.

A cewar rahotannin tsaro, akalla fursunoni 300 ne suka fece daga gidan yarin na Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja.

Idan baku manta ba, a ranar Talata 5 ga watan Yulin 2022 ne wasu ‘yan ta’adda suka kai mummunan farmaki kan gidan yarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel