Zafin Rashin Sulhu a Soyayya Ya Sanya Wani Mutum Kone Gidan Su Budurwarsa a Ogun

Zafin Rashin Sulhu a Soyayya Ya Sanya Wani Mutum Kone Gidan Su Budurwarsa a Ogun

  • Wani mutum mai shekaru 43 ya yi aikin dana-sani yayin da ya bankawa gidan su budurwarsa wuta
  • Wannan lamarin ya faru ne a jihar Ogun, inda mutumin ya bayyana dalilin kone gidan su budurwar tasa
  • ‘Yan sanda sun kwamshe shi, sun kuma bayyana matakin da suke dauka a kansa a wannan lokacin

Jihar Ogun - ‘Yan sanda a jihar Ogun sun yi ram da wani mutum mai shekaru 43, Hassan Yusuf bisa zargin bankawa gidan su tsohuwar budurwarsa, Busayo Falola wuta saboda matsalar soyayya.

An ruwaito cewa, wanda ake zargin ya kone gidan ne da ke lamba 127 a Old Scholar Palace da ke hanyar Igan a yankin Ago-Iwoye na karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar.

A cewar majiya, hakan ya faru ne bayan da budurwar tasa ta ki aurensa kana batun sulhu tsakaninsu ya ci tura, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An kashe malamin addinin Muslunci daidai lokacin buda baki a wata jiha

Yadda saurayi ya bankawa gidan su budurwarsa wuta
Jihar Ogun da ke Kudu maso Yamma | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru, daga bakin ‘yan sanda

Batun konewar na zuwa ne ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi a ranar Asabar cikin wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Oyeyemi, an kamo wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da wata mata mai shekaru 62 da aka ce itace mai gida, Adejoke Salau ta kai ofishin ‘yan sandan Iwoye.

Kakakin na ‘yan sanda ya ce, mata mai gidan ta ce, jama’a sun ji hayaniya a gidan da misalin karfe 1:15 na dare, inda da aka duba aka ga gidan na ci da wuta, rahoton Vanguard.

Ta kuma bayyana cewa, makwabta ne suka taimaka wajen shawo kan wutar tare da ceto masu hayan da ke ciki.

Da aka je ofishin ‘yan sanda, budurwar ta ce ta ga tsohon saurayin nata a lokacin da haka ya faru.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kame tsagerun 'yan bindiga 2 da suka addabi jihohin Arewa

Ya amsa laifinsa, ya fadi yadda ya aikata barnar

A lokacin da aka kamo tare da titsiye shi, Yusuf ya amsa laifinsa, inda yace ya yi hakan ne saboda gaza samun sulhu tsakaninsa da budurwar tasa.

A cewarsa, ya yi amfani da man fetur din N500 ne wajen yaryadawa gidan ta taga tare da jefa ashana cikin dakin.

Ya zuwa yanzu, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Frank Mba ya umarci a tattara Yusuf tare da mika shi sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda.

Ba wannan ne karon farko ba, a baya wani matashi mai shekaru 19 ya bankawa gidan su budurwarsa wuta saboda tangardar soyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel