Ba Zan Tsoma Baki a Harkokokin Gwamnatin Abba Gida-Gida Ba, Inji Rabiu Kwankwaso

Ba Zan Tsoma Baki a Harkokokin Gwamnatin Abba Gida-Gida Ba, Inji Rabiu Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana cewa, ba zai tsoma baki a mulkin Abba Gida-Gida na jam’iyyar NNPP ba
  • Rabiu Kwankwaso ne uban gidan Abba Gida-Gida na siyasa, ana sa ran zai shiga a yi mulkin nan dashi ka’in-da-na’in
  • Sai dai, ya yi karin haske, ya ce ko Abba ne ya yi kuskure zai sanar dashi, don haka babu ruwansa da batun tsoma baki

Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, ba zai tsoma baki a harkokin tafiyar da mulki a jihar Kano ba karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf; Abba Gida-Gida.

Kwankwaso dai shine uba gidan Abba Gida-Gida na siyasa, kuma ya kasance tsohon gwamnan Kano, jihar da ke Arewa maso Yamma a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Jama’a da yawa na ci gaba da bayyana damuwar cewa, akwai yiwuwar Kwankwaso ya ke tsoma baki a harkokin Abba Gida-Gida.

Ba zan shiga lamarin Abba Gida-Gida ba, Kwankwaso
Abba Kabir Yusuf, zababben gwamnan Kano | Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Sai dai, a tattaunawarsa da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce a matsayinsa na Bakano, zai kalubalanci gwamnatin Abba Gida-Gida a duk sadda ya ga wata matsala a cikinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabin Kwankwaso game da tsoma baki a mulkin Abba Gida-Gida

Da yake jawabi, Kwankwaso ya ce:

“Ko da mai sharanka ne ka nada a matsayin shugaba, to kada ka tsoma baki a lamarinsa. Idan ya nemi shawarinka sai ka bayar, amma idan bai nema ba, sai ka yi shuru.
“A lokacin da nake gwamna, na yi aiki da mutane irinsu Abba wadanda suka taimaka mini wajen cimma nasara.
“Wannan ne yasa muka zauna sannan muka duba dukkan mutanemmu kana muka zabi wanda muke tunanin idan Allah ya yarda, ba zai maimaita mulkin Ganduje ba."

Mun yi farin ciki da tumbuke tubakin Ganduje

Da yake karin haske game da gwamnati mai tafiya, Kwankwaso ya ce Kanawa sun ji dadin yadda aka tumbuke tubalin mulkin APC a jihar, Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa:

“Dukkanmu a jihar Kano mun yi farin cikin cewa Allah ya kore su, kuma muna addu’ar cewa Allah ya nesanta mu dasu. Duk wanda ke mulki a Kano, ko soja ne ko ma waye, ba za mu bari ya zama mara mutunci ba.
“Saboda haka, ko Abba ne zai yi shugabanci ba ko ma waye ne, za mu fada masa abin da yake na gaskiya, kuma a lokacin da ya kuskure, za mu fada masa.
“Abin da na sani shine cewa munanan abubuwan da suka faru a gwamnati mai tafiya za a gyara su.”

Idan baku manta ba, Abba gida-Gida ya ce duk wanda ya sayi filin gwamnati a Kano ya daina gini, gwamnati za ta dauki mataki

Asali: Legit.ng

Online view pixel