Kotun Musulunci Ta Yanke Wa Barawon Rake Hukunin Bulala 10 A Kano

Kotun Musulunci Ta Yanke Wa Barawon Rake Hukunin Bulala 10 A Kano

  • Alkali a wata kotun shari'ar musulunci da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano ya yanke hukunci ga wani mutum kan satar rake
  • Kotun ta yanke wa Ibrahim Musa Tofa hukuncin bulala 10 ne bayan ya amsa laifin kutse cikin gonar wani da tsakar dare ya saci rake
  • Har wa yau, alkalin kotun ya kuma umurci Tofa ya biya mai gonar kudin raken da ya shiga ya sace a gonarsa

Jihar Kano - Wata kotun shari'a da ke zamanta a karamar hukumar Kura na jihar Kano ta bada umurnin a yi wa wani Ibrahim Musa Tofa, bulala 10 saboda satar rake daga wani gona.

Wani Malam Ibrahim Isah Usman ne ya yi karar Tofa a kotu bayan mai gonar ya kama shi da taimakon wasu leburori saboda kutse cikin gonarsa cikin dare tare da sace rake.

Kotun shari'a
Kotun Musuluni Ta Yanke Wa Barawon Rake Hukunin Bulala 10 A Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Wanda ake zargi ya amsa laifinsa, ya kuma roki alkali ya masa afuwa

Bayan mai gabatar da kara ya karanto tuhumar da ake yi wa Ibrahim Musa Tofa, ya amsa laifinsa nan take ba tare da jayayya ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma roki alkalin kotun ya masa afuwa yana mai alkawarin ba zai sake aikata irin hakan ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Alkalin kotun ya zartar da hukunci nan take inda ya ce a yi masa bulala 10 sannan zai biya kudin raken da ya sata cikin dare a gonar.

An damke alkalan kotun shari'a a Kano saboda zargin wawushe kudin magada

A wani rahoton na daban, an kama wasu alkalai na shari'ar musulunci guda biyu tare da wasu ma'aikatan kotun musulunci su 17 kan zarginsu da wawushe kudin magada a jihar Kano.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, an kama mutanen su 19 ne kan zargin satar kudi har Naira miliyan 580.2.

Lauyan gwamnatin jihar Kano, Mista Zaharadeen Kofar-Mata ya ce hukumar da ke yaki da rashawa a Kano ta samu korafin badakalar da alkalan ke yi ne daga wurin ma'aikatar shari'a a ranar 20 ga watan Agustan shekarar 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel