An Kama Alkalan Kotun Shari'a A Jihar Kano Kan Zargin Cin Kudin Magada N580m

An Kama Alkalan Kotun Shari'a A Jihar Kano Kan Zargin Cin Kudin Magada N580m

  • Sabon badakala ya bayyana yadda Alkalan kotun shari'a biyu suka jagoranci satar kudin magada a Kano
  • Jami'an hukumar Shari'a a jihar sun kirkiri jabun takardu don samun daman kwashe kudade a asusun kotun
  • Bayan shekara biyu da tafka wannan satar, sun gurfana gaban kotu kuma an jefasu kurkuku

Kano - An damke wasu Alkalan kotun shari'ar Musulunci biyu da wasu ma'aikatan hukumar shari'a 17 ta jihar Kano bisa zargin rub da ciki da kudin magada.

Vanguard ta ruwaito cewa wadannan mutane su 19 sun shiga hannun hukuma ne bisa satar kudi har N580.2 million

An gurfanar da su gaban wani Alkalin kotun Majestiri mai lamba 14 Karkashin Mai Shari'a Mustapha Sa'ad Datti.

A karar da aka shigar kotun, ana zarginsu da hada baki da juna wajen aikata laifin cin Amana da Satar N580m.

Kara karanta wannan

Hotunan Shugaba Buhari Inda Ya Samu Lambar Yabon Wanzar da Zaman Lafiya a Afrika

kotun
An Kama Alkalan Kotun Shari'a A Jihar Kano Kan Zargin Cin Kudin Magada N96m Hoto: Arewa Radio 93.1
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda akayi a kotu

A zaman kotun, lauyan gwamnati Mr Zahraddeen Kofar-Mata ya bayyana cewa hukumar yaki da rashawan jihar Kano ta samu rahoton badakalar daga wajen ma'aikatar shari'a ranar 20 ga Agusta, 2021.

Ya ce tsakanin 2020 da 2021, daya daga cikin wadanda ake zargi Hussaina Imam, wacce mai ajiyan kudi ce a kotun daukaka kara ta hada baki da wasu mutum hudu wajen buga jabun takardan kotun.

Yace:

"Sun buga jabun sa hannun mutum biyu a akawunt na bankin kotun dake Stanbic IBTC bank 0020667440 kuma suka sace N484 million."

Ya kara da cewa tsakanin 2018 da 2021, sun sace kudi N96.2 million ta hanyar buga jabun takardun mutuwar wasu ma'aikatan gwamnati 15 don kwashe kudin fansho.

Yace:

"Hukumar fanshon jihar Kano ta sanya kudi N96.2 million cikin asusun bankin kotun daukaka kara ta shari'a."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mataimakin Shugaban Kasar Gambia, Badara Aliyu Joof, Ya Mutu A Ofis

"Wadannan mutane suka sace kudin da sunan kotunan shari'a takwas dake karkashin kular kotun daukaka karar ba tare da izinin gwamnati ba."

Lauyan ya ce wannan ya sabawa sashe na 97, 79, 315, 287 da 363 na dokar Penal Code, rahoton ya kara.

Lauyan wadanda ake zargi, Malam Garzali Datti ya bukaci kotun ta bada belinsu amma alkalin yayi watsi da bukatar.

Alkalin ya bada umurnin jefasu gidan gyara hali yayinda ya dage zaman kotun zuwa ranar 1 ga Febrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel