Bayan Shekara 8 Suna Zaman Dadiro, Wasu Masoya Sun Rabu Da Juna

Bayan Shekara 8 Suna Zaman Dadiro, Wasu Masoya Sun Rabu Da Juna

  • Wata soyayyar shekara takwas ta tunkuyi birji bayan masoyan sun rabu duk kuwa da suna ƴaƴa biyu tare
  • Budurwar da lamarin ya auku da ita, itace ta bayyana hakan yayin da ta koka kan yadda suka kwashe shekaru suna tare ba tare da ya aure ta ba
  • Masu amfani da yanar gizo sun tausayawa budurwar wacce aka nuna bidiyon ta tana tafiya kawai da kayanta

Wata budurwa ta rabu da saurayin ta bayan sun kwashe shekara takwas suna zaman dadiro.

Budurwar ta garzaya manhajar TikTok inda ta koka kan yadda soyayyarta ta ƙare yayin da take cewa da kayan jikinta kawai ta tsira.

Dadiro
Bayan Shekara 8 Suna Zaman Dadiro, Wasu Masoya Sun Rabu Da Juna Hoto: TikTok/mummie-g
Asali: TikTok

A cewar ta, sun haifi yara biyu tare sannan saurayin na ta ga ƙwace ƴaƴan ya kai su gaban iyayen sa.

Ta bayyana cewa tunda aure bai shiga tsakanin su ba gidan iyayenta zata koma da zama. Budurwar ta ƙara da cewa bai biya kuɗin sadakin ta ba sannan ko rana ba a taɓa sanya musu ba.

Kara karanta wannan

"Namiji Nake So" Wata Amarya Ta Ɓarke da Kuka Harda Hawaye Bayan Ganin Abinda Ta Haifa, Bidiyo Ya Girgiza Mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ta wanda ya nuna lokacin da take jan akwatin ta an yi wani rubuta a jikin sa mai cewa:

"Bayan mun yi zaman dadiro na shekara takwas da haiguwar yara 2, ba zoɓen aure, ba sadaki, ba aure.. Mun rabu sannan ya kai yaran gaban iyayen sa. Zan koma wajen iyaye na tare da kayan sanyawa ta."

Mutane sun yi maganganu a kai

@neema ta rubuta:

"Shiga cikin irin wannan halin akwai cin rai sosai. Amma na yiwa mahaifiyata rantsuwar cewa ba zan taɓa barin ƴaƴa na ba."

@Chosen one ta rubuta:

"Wannan sakarci ne. Wace uwa ce zata tafi ta bar ƴaƴanta? Ki koma ki ɗauko ƴaƴan ki ko kuma ki shiga garari duk lokacin da suka yi kuka."

@snezy50 ya rubuta:

"Ki daure ki tafi da yaran ki, mahaifiyata ta tafi ta barni har yau ina ganin laifinta kan yadda rayuwata ta kasance."

Kara karanta wannan

"Zan Koma Gida": Wata Yar Najeriya Ta Sharɓi Kuka A Bidiyo Mai Ratsa Zuciya, Ta Ce Ta Gaji Da Aiki A Dubai

@Dessy ya rubuta:

"Maza su ma iyaye ne. Ki koma gida ki fara gina kan ki sannan ki kwato yaranki ta hanyar shari'a."

Taron Biki Ya Tarwatse a Benin Bayan Amarya Ta Gano Ango Yana Da 'Ya'Ya 7

A wani labarin na daban kuma, wani taron biki ya tarwatse ana tsaka da shagalin biki bayan amarya ta gano wani sirrin angon.

Amaryar dai ta fusata lokacin da ta gano cewa angon ta ya sharara mata ƙarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel