Kare Ya Taya Uwar Dakinsa Aiki, Ya Debo Ruwa Sannan Ya Tafasa Mata a Bidiyo

Kare Ya Taya Uwar Dakinsa Aiki, Ya Debo Ruwa Sannan Ya Tafasa Mata a Bidiyo

  • Wani hazikin kare ya yadu a TikTok saboda yadda ya dunga dawainiya da uwar dakinsa wacce ke cikin halin rashin lafiya
  • Bayan karen ya taya ta dibo ruwa daga famfo, ya kuma tayata zubawa cikin buta sannan ya daura shi a kan rishon girki
  • Wannan abu da karen ya yi ya baiwa mutane da dama mamaki amma dama an san kare da tsananin biyayya ga ubangidansa

Wani kare mai tarin hikima ya yi fice a soshiyal midiya bayan wani bidiyo ya nuno shi yana taya uwar dakinsa aikin gida.

Shafin TikTok na @love.animal.9 ne ya wallafa bidiyon mai tsawon sakan 27, wanda ya nadi aikin hankali da karen ke yi.

Kare yana aikin debo ruwa
Kare Ya Taya Uwar Dakinsa Aiki, Ya Debo Ruwa Sannan Ya Tafasa Mata a Bidiyo Hoto: TikTok/@love.animal.9.
Asali: TikTok

A bidiyon, alamu sun nuna mai karen bata da lafiya domin dai an gano ta kwance a kan gado cikin wani daki.

Kara karanta wannan

Yaro Ya Tsaida Motoci Dake Zargadila Saboda Ya Tada Sallah Akan Titi a Turai, Vidiyon Ya Tada Hazo

Hazikin kare na taya uwar dakinsa aikin gida

Don haka, karen ya daurawa kansa aikin taya mamallakiyarsa da wasu ayyukan gida kamar dibo ruwa da kuma tafasa ruwan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Karen dai ya fara ne da dibo ruwa daga famfo. Ya dauki butan karfe a bakinsa sannan ya bude famfon ya cika shi da ruwa.

Bayan nan, sai karen ya dauki ruwan ya daura kan rishon girki mai aiki da lantarki, ya kunna shi sannan ya tafasa ruwan. Bayan nan, ya dauki butan ya ajiye a gaban uwar dakin nasa.

A halin da ake ciki, bidiyon ya burge mutane da dama da suka nuna mamakin cewa kare zai yi yin wannan aiki na hankali.

Sai dai wasu sun ce sam basu yi mamaki ba kasancewar ana yi wa karnuka lakabi abokan bin adam.

Kara karanta wannan

Ba dani ba: Jama'a sun kadu bayan ganin mutumin da ya reni zakanya tsawon shekaru 11

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@simbamimi.21 ta ce:

"Wannan bidiyon ya cancanci miliyoyin 'likes'. Karnuka sun fi komai."

@user7044929481411 ya yi martani:

"Karnuka sun fi komai."

@elnure84 ya ce:

"Wannan gaye mai cike da hikima haka. Zai zamo abokina wanda zai kasance tare da ni a koda yaushe."

@zuhrauaysova1960 ya yi martani:

"Ainahin masu bauta. Suna bautawa har karshen rayuwarsu. Halitta mafi hankali."

Budurwa ta baje kolin gidan da take haya kan miliyan 4.8, bidiyon ya dauka hankali

A wani labari na daban, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiypn gidan gaya da wata budurwa tace tana biyan miliyan N4.8 duk shekara.

Gidan wanda ke a yankin Lekki na jihar Lagas ya tattara duk wasu abubuwan more rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel