Gwamnan Jihar Sakkwato Ya Rasa Kwamshinan Harkokin Addinin Musulunci

Gwamnan Jihar Sakkwato Ya Rasa Kwamshinan Harkokin Addinin Musulunci

  • Dukkan mai rai mamaci ne, Allah ya yi wa kwamishinan harkokin Addinai, Alhaji Usman Suleiman, rasuwa
  • Rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ranar Jumu'a yana da shekaru 72 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Gwamna Aminu Tambuwal ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da ɗaukacin mazauna Sokoto

Sokoto - Kwamishinan harkokin Addinai na jihar Sakkwato, Alhaji Usman Suleiman (Ɗanmadamin Isa), ya riga mu gidan gaskiya.

Ɗanmadamin Isa, ya rasu ne jiya Jumu'a a Asibitin koyarwa na jami'ar Usman Ɗanfodio da ke Sakkwato bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, yana da shekaru 72.

Gwamna Aminu Tambuwal
Gwamnan Jihar Sakkwato Ya Rasa Kwamshinan Harkokin Addinin Musulunci Hoto: Aminu Tambuwal
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa har zuwa numfashinsa na karshe, Marigayin ya rike kujerar shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar, daga bisani Tambuwal ya naɗa shi a matsayin kwamishina.

Marigayi Alhaji Usman Suleiman ya kasance tsohon kwamishinan ayyuka da Sufuri, tsohon kwamishinan raya karkara, sannan kuma kwamishinan harkokin Addinai, mukamin da ya rasu yana kai.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Manyan Jiga-Jiganta a Jihohi 5, Ta Ɗauki Mataki Kan Wani Gwamnan Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kafin rasuwarsa, ya kasance shugaban kamfanonin USDANIS Nigeria Limited, USDANIS Petroleum Resources limited da kuma Aminci Bureau De – Change.

An tattaro cewa marigayin mutum ne mai juriya da aiki kuma mai son addini, hakan ya ja hankali Gwamna Tambuwal ya maida shi ma'aikatar kula da harkokin addinai a matsayin kwamishina.

Tambuwal ya yi ta'aziyya ga iyalansa

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai, Muhammad Akibu Dalhatu, ya rabawa manema labarai, Gwamna Tambuwal ya miƙa ta'aziyya ga iyalan marigayin da ɗaukacin mazauna Sakkwato.

A saƙon ta'aziyyar, gwamnan ya roki Allah SWT, "Ya gafartawa marigayin kuma ya sa mutuwar ta zame masa huta, kana ya baiwa iyalansa da sauran mutanen jiha kwarin guiwar jure wannan rashi."

Danmadamin Isa ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya da jikoki da dama, daga cikin 'ya'yansa har da Alhaji Jamilu Usman Danmadamin Isa, fitaccen ɗan kasuwa a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kama wasu da ke sace yara da sunan za su kaisu gidan marayu a jihar Arewa

Tuni aka gudanar da Sallar Jana'iza ga mamacin a gidan da ke Anguwar Polo Club da ke Sakkawato, Allah ya masa rahama, Ameen.

Allaja ya yi wa jigon PDP rasuwa

A wani labarin kuma An shiga Yanayin Tashin Hankali Yayin Da Jigon Jam'iyyar PDP Ya Mutu A Hadarin Mota

Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Gombe, Nasiru Nono, ya rasa rayuwarsa a wani a haɗarin mota da ya rutsa da shi ranar Alhamis da ta gabata..

Asali: Legit.ng

Online view pixel