Nasiru Nono: Tashin Hankali Yayin Da Jigon Jam'iyyar PDP Ya Mutu A Hadarin Mota

Nasiru Nono: Tashin Hankali Yayin Da Jigon Jam'iyyar PDP Ya Mutu A Hadarin Mota

  • Jihar Gombe ta rasa daya cikin tsaffin kakakakin majalisar ta a ranar 23 ga watan Maris, mai suna Nasiru Nono
  • Nono, jigon jam'iyyar PDP a jihar ya rasu a hadarin mota a kan babban titin Abuja zuwa Keffi
  • Tsohon kakakin majalisar yana tare da Hon. Haruna Usman Fada, tsohon dan majalisar jihar, a cikin motar lokacin da hadarin ya faru

Nasiru Nono, tsohon kakakin majalisar jihar Gombe, ya rasu a hadarin mota kan babban hanyar Abuja-Keffi, ranar Alhamis, 23 ga watan Maris.

Tsohon sakataren jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Gombe, Buba Shanu, ya tabbatarwa The Punch rasuwar Nono, abin da ya ce labari ne mara dadi.

Nasiru Nono
Nasiru Nono: Tashin Hankali Yayin Da Jigon Jam'iyyar PDP Ya Mutu A Hadarin Mota. (Nasiru Nono)
Asali: UGC

A cewar Shanu, Nono yana tafiya ne tare da tsohon dan majalisar dokokin jihar, Hon Haruna Fada.

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

"Shi (Nono), ya rasu a mummunan hadarin mota kan babban hanyar Abuja-Keffi. Yana tafiya ne tare da Hon. Usman Fada, tsohon dan majalisa wanda ya tsira kuma yana karbar magani."

Nono ya yi fice cikin kakakin majalisun jiha a 2018 lokacin da aka ce wasu yan majalisa sun sace masa sandan iko.

Amma, daga bisani yan sanda sun gano sanda a bayan harabar Kotun Ma'aikatu na Kasa a jihar, da aka tunanin wasu da ba a san ko su wanene ba suka yarda.

Ya nemi zama sanata na Gombe ta Tsakiya a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a shekarar 2019.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel