'Yan Sanda Sun Kwamushe Wasu Masu Satar Yara da Sunan Suna Kai Su Gidan Marayu

'Yan Sanda Sun Kwamushe Wasu Masu Satar Yara da Sunan Suna Kai Su Gidan Marayu

Niger - Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bankado wasu bata-gari da ke sace yara tare da fakewa da sunan gidan marayu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana bankado gidan tare da kama mutane biyu da ake zargin su ke gudanar da harkallar sace yaran.

Jami'an yan sanda rike da bindigogin
'Yan Sanda Sun Kwamushe Wasu Masu Satar Yara da Sunan Suna Kai Su Gidan Marayu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wadanda aka kaman sun hada da Saviour Ebuka mai shekaru 20 da kuma Mary Peter ‘yar shekara 25 a yankin Tunga-Maje a karamar hukumar Gwagwalada da ke kusa da babban birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewa, kama wadannan mutane ya zo ne bayan samun rahoton sun sace wasu yara biyu, kamar yadda aka kai rahoto a ofishin ‘yan sanda na Suleja a jihar Neja.

Karin bayani na nan tafe...

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Asali: Legit.ng

Online view pixel