Rikici Ya Barke Tsakanin Wakilan Jam'iyyar APC Da PDP A Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe

Rikici Ya Barke Tsakanin Wakilan Jam'iyyar APC Da PDP A Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe

  • Riciki ya barke tsakanin wakilan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da All Progressives Congress, APC, bayan da PDP ta zargi APC da tura wakilai da yawa cibiyar tattara sakamakon zabe a Jihar Ogun
  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta kuma zargi jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki da dakile jiga-jiganta da kuma hana mamboninta yin zabe
  • Jami'an hukumar zabe da ke aikin tattara sakamakon zaben ya bukaci jam'iyyar APC ta zabi wakili daya a cikin guda ukun da ya ke sasanta lamarin

Jihar Ogun - Wakilan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, sun yi arangama a ranar Lahadi a cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun na 2023, rahoton The Punch.

Rikicin ya fara ne lokacin da wakilin PDP, Sunkanmi Oyejide, ya tashi ya nuna adawa da wakilcin APC na gabatar wakilai uku da suka yi.

Kara karanta wannan

Fargaba Yayin Da APC, NNPP Suka Umurci Magoya Bayansu Su Mamaye Cibiyoyin Tattara Kuri'un Zabe A Kano

Zaben Najeriya
Masu kada kuri'a a rumfar zabe. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Oyejide ya kuma koka da cewa da gangan APC ta kawo cikas ga jiga-jigan jam’iyyar a jihar domin hana wa ‘ya’yanta hakkokinsu.

Ya ce:

“Idan ka lura da kyau, jam’iyya mai mulki ta dakile manyan PDP tare da hana wa mambobinmu hakkokinsu.
“Muna son ku yi nazari mai zurfi kuma ku bincika. Dole ne tsarin ya kasance a bayyane."

Sai dai wakilin jam’iyyar APC mai suna Adelani bai amince da wannan zargi na wakilin PDP ba.

Lamarin ya janyo tsaiko na kimanin mintuna 15 kafin al'amura su dawo.

Jami’in tattara sakamakon zabe na hukumar zabe mai zaman kanta na jihar, Farfesa Kayode Adebowale, a yayin da yake sasanta rikicin, ya bukaci jam’iyyar ta zabi daya daga cikin wakilai uku na APC a cibiyar.

Ya kuma caccaki wakilin PDP a kan ikirarin dakile jiga-jiganta, yana mai cewa, an bi ka’ida.

Kara karanta wannan

Zaben Ranar Asabar: Jigon Jam'iyyar PDP Ya Yi Murabus Daga Awanni Kadan Kafin Zabe, Ya Bayyana Dalili

Adebowale ya ce:

“Ba mu san wuraren da haka ta faru ba. An bi ka’ida.”

An ci gaba da atisayen ne yayin da karin jami’an tattara sakamakon kananan hukumomin ke cigaba da gabatar da sakamakon.

Bidiyon Kwamishina a Jihar Bauchi yana rabon sabbin naira gabanin zaben gwamna

A wani rahoton, kun ji cewa wani bidiyo ya yadu a soshiyal midiya inda aka gano wani da aka ce kwamishinan matasa da wasanni na jihar Bauchi, Adamu Manu Soro ne yana rabon naira ga mutane gabanin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel