Dan Takarar LP da Aka Sace Ya Kubuta, Ya Faɗi Abinda Ya Gani Wurin Yan Bindiga

Dan Takarar LP da Aka Sace Ya Kubuta, Ya Faɗi Abinda Ya Gani Wurin Yan Bindiga

  • Ɗan takarar majalisar dokoki a inuwar LP da mahara suka sace ya shaki iskar yanci bayan shafe kwanaki a hannunsu
  • Boma Kasim-Agida, ya ce tun da suka ɗauke shi babu wanda ya ce masa komai amma ya ga abinda suka aikata
  • Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan Ribas ta ce suna kan bincike game da lamarin a halin yanzu

Rivers - Ɗan takarar majalisar dokokin jihar Ribas mai wakiltar mazaɓar Ahoada ta yamma karkashin inuwar Labour Party, ya shaki iskar yanci bayan an yi garkuwa da shi.

Boma Kasim-Agida, wanda ya shiga hannun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a kofar shiga Otal dinsa, yana hanyar dawowa daga Ralin kamfen da ya gudana a Ahoada ta yamma ranar Talata.

Taswirar jihar Ribas.
Dan Takarar LP da Aka Sace Ya Kubuta, Ya Faɗi Abinda Ya Gani Wurin Yan Bindiga Hoto: channelstv
Asali: UGC

Me ya faru bayan maharan sun tafi da shi?

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Hadimin Gwamnan Arewa, Bayanai Sun Fito

Da yake labarta abubuwan da ya gani a sansanin masu garkuwa da mutane, Kasim Agida ya ce kwana uku ya kwashe a wurin maharan da suka sace shi amma ba su ce masa komai ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa da Channels tv ta rahoto, ɗan siyasan ya ce:

"Na kwashe kwanaki uku a tare da su, daga ranar Talata zuwa Jumu'a, kuma ba su ce da ni komai ba, abinda na fahimta kamar suna jiran umarni ne daga wani."
"Ba'a biya ko naira ɗaya da sunan kuɗin fansa ba, sun ɗaure mun ido kana suka tafi da ni suka aje ni a wani wuri kusa da titin Amasoma da ke jihar Bayelsa."

Da yake karin haske kan lamarin, ɗan takarar majalisar na LP ya nuna yaƙinin cewa ɗage zabe da mako ɗaya da aka yi ya taimaka matuka gaya wajen kubutarsa daga hannun masu garkuwa.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata, EFCC Ta Gama Shirin Kama Gwamnonin Jihohin da Za Su Bar Ofis

"Nasara ta Allah ce ga shi an ɗage zaɓe, ina tunanin hakan ya taimaka har na samu na kubuta," inji shi.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntube ta, jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta ce har yanzun suna kan gudanar da bincike kuma babu wanda aka kama kawo yanzu.

A wani labarin kuma Jami'an Tsaro Sun Kama Mataimakin Shugaban APC Na Jiha Kwana 2 Gabanin Zabe

An ce dakarun yan sanda sun cafke shi ne bisa umarnin mataimakin gwamnan jihar Edo, Honorabul Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel