Jami'an Tsaro Sun Kama Mataimakin shugaban APC a Jihar Edo

Jami'an Tsaro Sun Kama Mataimakin shugaban APC a Jihar Edo

  • Jami'an tsaro sun cafke mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Edo, Jarret Tenebe, kwana 2 gabanin zabe
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kama jigon siyasar ne a mahaifarsa, Ikabigbo, yankin karamar hukumar Etsako ta yamma
  • Har kawo yanzun babu cikakken bayani kan inda yake ko dalilin kama shi daga hukumar 'yan sandan jihar

Edo - Kwanaki biyu gabanin zaben mambobin majalisar dokoki a jihar Edo, an damƙe mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar, Jarret Tenebe.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ana zargin jami'an tsaro sun kama mataimakin shugaban APC ne bisa umarnin mataimakin gwamnan Edo, Honorabul Philip Shaibu.

Taswirar jihar Edo.
Jami'an Tsaro Sun Kama Mataimakin shugaban APC a Jihar Edo Hoto: vanguard
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa an kama Mista Tenebe ne a garinsu, Ikabigbo, ƙaramar hukumar Etsako ta yamma kuma sun tafi da shi zuwa wurin da ba'a sani ba kawo yanzu.

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

Tenebe ya yi kaurin suna kuma fitacce ne wajen tattara wa jam'iyyar APC magoya baya da masu kaɗa kuri'a kuma ya kasance ɗan a mutun Kwamaret Adams Oshiomhole.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani bidiyo da ya watsu a kwanan nan, mataimakin shugaban APC ya caccaki mataimakin gwamnan Edo kan manyan batutuwa masu sarƙaƙiya da dama.

A wani taron manema labarai da ya gudana a Benin City ranar Talata, jam'iyyar APC ta zargi gwamnatin Edo na shirya manaƙisar magudin zabe ta hanyar amfani da 'yan daba ranar Asabar.

Wane hali ake ciki game da kama jigon APC?

Shugaban APC na jiha, Kanal David Imuse mai ritaya da mataimakin jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar, Ofure Osehobo, sun tabbatar da lamarin cafke Tenebe.

Tribune ta ce har kawo yanzun rundunar 'yan sanda ba ta ce komai ba yayin da aka tuntubi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar Edo, Chidi Nwabuzor, bai ɗaga kiran waya ba.

Kara karanta wannan

An Shawarci Bola Tinubu Ya Bai Wa Faleke Shugaban Ma’aikata

DSS Sun Kama Mutum 2 Kan Shirin Haddasa Rikici Yayin Zaben Gwamnan Kano

A wani labarin kuma DSS Ta Kama Mutum 2 Da Ke Shirin Tada Zaune Tsaye Yayin Zaben Gwamna a Kano

Peter Afunanya, mai magana da yawun DSS, ya ce dakarun sun yi ram da mutanen da zargin kulla makircin ta da rikici a lokacin zaben ranar Asabar.

Ya kuma bayyana sunayen waɗanda ake zargin da kuma irin laifukan da suka aikata na ta da zaune tsaye a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel