Wata Ma'aikaciyar Lafiya Ta Yanke Jiki Ta Faɗi Tana Tsaka da Aiki a Zamfara

Wata Ma'aikaciyar Lafiya Ta Yanke Jiki Ta Faɗi Tana Tsaka da Aiki a Zamfara

  • Rai bakon duniya, Allah ya yi wa wata ma'aikaciyar jinya rasuwa yayin da take cikin sauke nauyinta a Asibiti a Zamfara
  • Mai magana da yawun Asibitin, Auwal Usman, ya ce Asma'u ta fito aiki lafiya kalau amma ba zato ta yanke jiki ta faɗi
  • Ya ce Likitoci sun yi bakin kokari domin ceto rayuwarta amma sa'i ya yi, nan take rai ya yi halinsa

Zamfara - Asmau Lawali Bungudu, Ma'aikaciyar jinya watau Nurse a Asibitin Ahmed Sani Yariman Bakura da ke Gusau, jihar Zamfara ta riga mu gidan gaskiya.

Tribune Online ta rahoto cewa Asmau ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi yayin da take tsaka da aikinta a Asibitin.

Asmau Lawali Bungudu.
Ma'aikacin jinya a Asibiti, Asma'u ta rasu Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa Marigayya Asma'u ta fito wurin aiki lafiya kalau da safiyar Laraba, amma awanni bayan fara aikin ranar aka tabbatar da rai ya yi halinsa.

Kara karanta wannan

Asiri Zai Tonu, Shugabannin Jam’iyyar APC Na Fada Kan Zargin Cinye Kudin Kamfe

Kakakin Asibitin, Auwal Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce Asma'u na cikin aikinta kuma ta gwada hawan jinin kusan majinyata 30 kafin daga bisani ta faɗa wa Likita tana jin ba daɗi a zuciyarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, nan take bayan ta gaya wa Likita haka, ta yanke jiki ta faɗi, Likitoci sun yi iya bakin kokarinsu domin su ceto rayuwarta amma tace ga garinku nan

"Kwararrun Likitoci sun yi kokarin ceto rayuwarta amma nan take rai ya yi halinsa," inji PRO

Auwal Usman ya kara da shugabannin Asibitin karkashin jagorancin Dakta Usman Muhammad Shanawa, sun miƙa gawar mamaciyar hannun 'yan uwanta.

Wani ɗan gidansu marigayya Asma'u ya tabbatar da cewa ta bar gida lami lafiya da safe, ta tafi Asibitin da take aiki a matsayin ma'aikaciyar jinya.

Daily Post ta rahoto ya ce:

Kara karanta wannan

Rashin Kudi Ya Sa An Gaza Binne Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

"Za'a mata Sallah jana'iza yau da misalin karfe 5:00 na yamma a kofar gidan Malam Abdurrahman da ke Magama a garin Bungudu."

Na'ibin limamin masallacin Sultan Bello ya rasu

A wani labarin kuma Allah Ya Yiwa Na'ibin Limamin Masallacin Sultan Bello Rasuwa

Mallam Ibrahim Isa ya rasu ne a Asibitin cikin garin Kaduna da safiyar ranar Laraba 15 ga watan Maris, 2023.

A wata sanarwa da kwamitin masallacin ya fitar, ya ce za'a yi wa mamacin jana'iza bayan Sallar Azuhur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel