Shugaba Buhari Ya Rantsar da Mutane 7 da Ya Naɗa Mukamai

Shugaba Buhari Ya Rantsar da Mutane 7 da Ya Naɗa Mukamai

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa mambobin tafiyar da ICPC shahadar kama aiki bayan sabunta naɗinsu
  • Bikin rantsuwar mambobin 7 ya gudana ne a fadar shugaban kasa jim kaɗan gabanin fara taron FEC na mako-mako
  • Nan da watanni 2 da 'yan kwanaki, gwamnatin Buhari zata miƙa mulki ga sabuwar zababbiyar gwamnatin Tinubu

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rantsar da mutum Bakwai da ya sabunta naɗinsu a matsayin mambobin majalisar gudanarwa na hukumar yaƙi da masu cin hanci (ICPC).

An tattaro cewa an gudanar da bikin rantsuwar kama aikin mambobin a Council Chambers da ke fadar shugaban kasa a Abuja ranar Laraba.

Fadar shugaban kasa.
Bikin rantsarwa gabanin taron FEC a Aso Rock Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Mutanen guda 7 sun karɓi shahadar kama aiki ne jim kaɗan gabanin fara taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) na mako-mako bisa jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da farashin kayayyaki ya kara hawa a Najeriya daidai karancin Naira

Babban mai taimaka wa shugaban kasa ta fannin harkokin kafafen sada zumunta, Buhari Sallau, ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sallau ya rubuta cewa:

"Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rantsar da mambobi 7 na majalisar gudanarwa ta ICPC kana ya jagoranci taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) a fadar gwamnatinsa ranar 15 ga watan Maris, 2023."

Jerin sunayen mutanen da Buhari ya rantsar

Mambobin da Buhari ya rantsar sun haɗa da, Mai shari'a Adamu Bello (Mai ritaya) daga jihar Katsina, Hannatu Mohammed daga Jigawa, Olubukola Balogun daga Legas da Obiora Igwedibia daga jihar Anambra.

Sauran su ne, Dakta Abdullahi Saidu daga jihar Neja, Yahaya Umar Dauda daga jihar Nasarawa da kuma Grace Chinda daga jihar Ribas.

A ranar 29 ga watan Mayu, 2023, shugaban ƙasa Buhari zai miƙa ragamar mulkin Najeriya ga sabuwar gwamnati karkashin shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Jerin Zabbabun Sanatoci 5 Da Ke Neman Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bayyana

A wani labarin kuma PDP Ta Fusata a Arewa, Ta Dakatar da Tsoffin Ministoci 2 da Wasu Manyan Jiga-Jigai 5

Babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa watau PDP ta dauki matakin dakatarwa kan wasu tsoffin ministoci 2 da mambobi 5 a jihar Kebbi.

Amma lamarin ya zo da wata sarƙaƙiya da ruɗani yayin da shugaban PDP na Kebbi, ya ce ba zai taba yuwuwa ba, zasu shawo kan komai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel