An Kama Bokan Da Ke Yi Wa Mutane Alkawarin 'Azirta' Su Ba Tare Da Amfani Da Sassan Jikin Dan Adam Ba A Edo

An Kama Bokan Da Ke Yi Wa Mutane Alkawarin 'Azirta' Su Ba Tare Da Amfani Da Sassan Jikin Dan Adam Ba A Edo

  • Wani bokan bogi ya shiga hannun jami'an tsaro biyo bayan zarginsa da aikata fashi da makami da kuma damfara
  • Wanda ake zargin, ya bude Facebook inda ya ke ikirarin cewa shi boka ne kuma yana tsafin kudi ba tare da amfani da sassan mutane ba
  • Da ya ke shaidawa yan jarida yadda abin ya faru ya ce abokan sa ne da suka dade suna harkar suka janyo shi ciki kuma yayi nadamar biye musu

Jihar Edo - Jami'an yan sanda a Jihar Edo ta damke wani boka, Frank John mai shekaru 25, bisa zargin yunkurin kisan kai da kuma fashi da makami, rahoton Daily Trust.

Kakakin yan sanda, SP Chidi Nwanbuzor, ya ce wanda ake zargin da abokan aikinsa (masu yawa) sun bude shafuka a kafar sadarwa ta Facebook, yana ikirarin boka ne shi kuma zai iya sa mutum ya zama attajiri ba tare da amfani da jini ko sassan jikin dan adam ba.

Kara karanta wannan

"Ya Yi Wuff Da Tsaleliyar Budurwa": Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Ya Wuff Da Kyakkyawar Yarinya Ya Haddasa Cece-Kuce

Taswirar Jihar Edo
An kama wani boka da ya yi ikirarin zai azirta wasu ba tare da tsafi da sassan jiki ba a Edo. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce an yaudari wadanda abin ya shafa, Shittu Kazeem da Sunday Christian, suka fara hira da shi ta WhatsApp da Facebook bisa alkawarin za su yi kudi.

Ya ce wanda tsautsayin ya fada wa sun ziyarci wanda ake zargin a Igara da ke karamar hukumar Akoko-Edo daga jihohin Bayelsa da Rivers da nufin ya azurta su amma sai ya kwace mu su kudade ta karfi tare da barin su da yankan takobi.

Ya yi bayanin cewa:

''Shitu ne ya fara zuwa wajen bokan a Igarra don ayi masa tsafin kudi. Wanda ake zargin ya kai shi daji, ya kwace katin cirar kudin ATM dinsa ta karfi hade da lambar sirri da kuma cire kudi daga asusunsa.
''Na biyu da abin ya shafa, Christian, an kai shi daji da nufin ayi masa wankan asiri inda aka masa dukan tsiya tare da saran shi da takobi a kansa da fuska. Shima sun kwace katin cirar kudin a hannunsa ta karfi hade da lambar sirri da niyyar cirar kudi daga asusun ajiyarsa.''

Kara karanta wannan

Na Kashe Mutane Sama Da 15 A Katsina Amma Ina Neman Afuwa, Ɗan Ta'adda Mai Shekaru 28 Da Dubunsa Ta Cika

Yadda aka kama wanda ake zargin

Ya cigaba da cewa wanda ake zargin yana kan hanyarsa ta dawowa daga banki ne lokacin da yan sanda suka dakatar shi suka kuma tsinci takarda dauke da lambar asusu da kuma lambobin sirri wanda hakan ya janyo zargi.

Chidi ya ce wanda ake zargin ya tabbatar da bude asusun Facebook da ikirarin shi boka ne wanda ke azurta mutane ba tare da amfani da sassan jikin mutune ko jini ba, ya kara da cewa abokan aikinsa sun gudu kafin yan sanda su isa dajin.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, wanda ake zargin ya ce ya bude Facebook yana ikirarin boka ne shi da ke azurta mutane ba tare da amfani da sassan mutane ko jininsu ba, sai dai akuya da raguna.

Ya ce:

''Lokacin da Shittu ya kira ni daga Jihar Bayelsa cewa yana son tsafin kudi, na fada masa farashin N35,000 ne. Ya yi alkawarin zai zo idan ya hada kudin saboda shi matukin adaidata sahu ne.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Yadda Najeriya Tayi Asarar Naira Tiriliyan 20 a Yunkurin Canza Kudi

''Ya zo ranar Laraba da ta wuce don ayi tsafin. N35,000 muka nema amma ya ce bai shirya ba yazo ne kawai ya ga yadda ake aikin.
''Shitu ya ce yana da N18,000 a asusunsa. Ya bani katin cirar kudi da lambar sirri ya kuma ce in ciri 15,000 daga cikin N18,000.
''Ina hanyar ciro kudin ne jami'an sintiri suka kama ni da suka ganni dauke da katin cirar kudi da kuma takarda dauke da lambar sirri tare da ni.''

Ya kara da cewa:

''Ba ni da ikon mayar da wani mai kudi. Ni mai aikin ruwa ne kuma a Lagos na ke amma lokacin da na dawo gida ban samu aiki ba. Abokaina a kauye suka bani shawara in shiga Yahoo saboda sun dade suna yi. Na yi nadamar shiga cikinsu.''

Na kashe fiye da mutum 15 A Katsina, Dan Ta'adda Dan Shekara 28 Da Aka Kama

A wani labarin, yan sanda sun kama wani dan bindiga, Sulaiman Iliyasu da ya amsa cewa ya halaka a kalla mutane 15 a hare-haren da suka kai a Katsina.

Kara karanta wannan

Yar Haya Ta Kashe Mai Gida Ta Hanyar Matse 'Ya'yan Marainansa A Ogun

Vanguard ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne yayin da aka yi holensa a hedkwatar yan sanda na Katsina a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel