Yar Haya Ta Kashe Mai Gida Ta Hanyar Matse 'Ya'yan Marainansa A Ogun

Yar Haya Ta Kashe Mai Gida Ta Hanyar Matse 'Ya'yan Marainansa A Ogun

  • Wata yar haya ta kashe mai gidan da ta ke haya har lahira ta hanyar jan mazakutarsa biyo bayan hatsaniya
  • Mamacin ya fadi bayan matar ta ja mazakutarsa inda aka garzaya da mamacin asibitin inda likita ya tabbatar da mutuwarsa
  • Jami'an yan sanda sun cafke wacce ake zargin Ifeoma Ossai, tare da alkawarin fada bincike da kuma gurfanar da it

Ogun- Jami'an yan sandan Jihar Ogun sun kama wata mata mai shekaru 33, Ifeoma Ossai, bisa zargin kashe maigidan da ta ke haya dan shekara 50, Monday Surulere Oladele, saboda wata karamar hatsaniya.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa wadda ake zargin ta shiga hannu biyo bayan rahoton da aka shigar a ofishin Sango Ota ta hannun wani Olaleye Taiwo.

Yar Haya
Yar haya da ake zargin ta kashe mai gidan haya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Wata Mata Mai Shayarwa Ta Jefar Da Jinjirinta Yayin Tserewa Daga Yan Bindiga A Neja

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Taiwo ya shigar da kara a ofishin yan sanda cewa dan uwansa, Oladele, ya yi fada da yar hayarsa akan takardar wuta, kuma a garin haka, ita yar hayar ta kama mazakutarsa da kuma dinga jan shi da ita.

A cewar sa, maigidan ya fadi a kasa kuma aka garzaya da shi babban asibiti, da ke Ota, inda ya mutu.

Martanin yan sanda

Mai magana da yawun yan sanda, Abimbola Oyeyemi ranar Talata bayan shigar da rahoton, DPO na ofishin Ota, Saleh Dahiru, ya tura jami'ai wajen inda suka kama wadda ake zargi aka kuma tsareta don bincike.

''Da ake tuhumarta, wadda ake zargin ta yi ikirarin cewa marigayin ya bukaci da ta biya kudin wuta, amma sai ta ce ba zata biya ba har sai an jona mata ruwa a bangarenta kamar yadda maigidan ya alkarwarta kafin ta tare cewa ba zata biya kudin wuta ko wani abu ba.

Kara karanta wannan

Rashin Kudi Ya Sa An Gaza Binne Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

''Wannan ya janyo cecekuce tsakanin su wanda ya sanya wadda ake zargin ta kama mazakutar marigayin da ja shi da ita.
''Marigayin ya fadi, kuma aka yi gaggawar kai shi asibiti amma sai likitan da ke aiki ya bayyana mutuwarsa,'' in ji Oyeyemi.

Ya ce an ajiye gawar a dakin adana gawa na asibitin don cigaba da bincike.

Oyeyemi ya ce kwamishinan yan sanda, Frank Mba, ya umarci a mayar da wadda ake zargi zuwa sashen binciken manyan laifuka don fadada bincike da kuma gurfanar da ita gaban kotu.

Amoketun sun kama wani mutum dauke da tsabbar sabbin kudi N250,000 na bogi

A wani labarin mai kama da wannan, jami'an hukumar tsaro na kudu maso yamma wato Amotekun sun kama wani mutum, Celestine da takardun naira na bogi da adadin su ya kai N250,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel