An Tsinci Gawar Malamin Jami'a da Shaida Burna Wuƙa a Jikinsa a Kuros Riba

An Tsinci Gawar Malamin Jami'a da Shaida Burna Wuƙa a Jikinsa a Kuros Riba

  • An tsinci gawar Farfesa a fannin kwas ɗin kimiyyar siyasa, Farfesa Felix Akpan, na jami'ar Kalaba (UNICAL)
  • Kakakin yan sanda a jihar Kuros Riba, ya ce tuni suka kama wani abokinsa da ake zargi, suna kan bincike
  • Wata majiya daga Anguwar da lamarin ya faru ta bayyana yadda abun ya afku tun daga farko

Cross River - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Kuros Riba ta tabbatar da gano gawar wani Farfesan Kimiyyar siyasa daga jami'ar Kalaba, Farfesa Felix Akpan.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, SP Irene Ugbo, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an tsinci gawar ne ranar Lahadi.

Taswirar jihar Kuros Riba.
An Tsinci Gawar Malamin Jami'a da Shaida Burna Wuƙa a Jikinsa a Kuros Riba Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

A cewarsa, an gano gawar ɗauke da raunukan burma wuka a wurare da dama a gidan mamacin da ke Plot 181, garin Duke kusa da rukunin gidajen jiha a Kalaba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Saura kwanaki zabe, an sace dan takarar majalisar dokokin wata jiha

Mista Ugbo ya ce sun fara kama waɗanda ake zargi da hannu yayin da jami'ai suka buɗe shafin bincike kan kisan, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin yan sandan ya ce:

"Akwai wanda ake zargi tsare a hannun mu, wanda ya yi ikirarin abokin mamacin ne (Farfesa Akpan), ya ce bai san abinda ya faru ba ko wanda ya soka masa wuka har ya mutu."
"Tuni tawagar bin diddigi suka fara aiki, nan ba da jimawa ba zamu tono tushen lamarin ta hanyar gano asalin wanda ya aikata kisan."

Akwai wanda ake zargi - Majiya

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta, ta ce mamacin, tsohon shugaban sashin kula da jin daɗin daliban jami'ar UNICAL ya yi wani baƙo ranar Asabar.

Baƙon ya tafi da sanyin safiyar ranar Lahadi zuwa Akampka kafin daga bisani a gano gawar farfesan.

Kara karanta wannan

Kisan Kai: Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Majalisar Tarayya Na Birni a Arewa Ruwa a Jallo, Sun Sa Lada N1m

NAN ta rahoto majiyar na cewa:

"Ya yi wani baƙo namiji, wanda ya zo masa ziyara a ƙarshen mako, amma mutumin ya tafi da sanyin safiyar Lahadi kamar karfe 5:00 na Asuba."
"Wata da ke zama a Anguwa ta ce ta ji ƙara daga gidan a wannan rana da wannan baƙon, wanda aka tabbatar abokinsa ne, ya bar gidan kuma ta yi hanzarin faɗawa makota ƙarar da ta jiyo."
"Bisa sa'a bakon ya manta wani abu da ya sa ya dawo gidan domin ya ɗauka, daga nan aka cafke shi, muka tafi da shi gidAn Farfesa Akpan, inda muka gano gawarsa da tabon soka wuka."

Sojojin Najeriya sun yo ƙasa a duniya

A wani labarin kuma Rundunar Sojin Najeriya Ta Hau Matsayi Na 36 Daga Cikin 145 Mafi Karfin Wuta a Duniya

A sabon rahoton da aka fitar na kasashe masu karfin sojoji 145 a duniya, Najeriya ta samu koma baya daga matsayin da take a 2022.

Kara karanta wannan

Sakataren PDP da Wasu Jiga-Jigai Sun Yi Murabus, Jam'iyyar Ta Maida Martani Mai Zafi

Haka zalika Najeriya ta koma na hudu daga matsayi na uku da take bara a jerin ƙasahen nahiyar Afirka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel