Rundunar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Ɗan Majalisar Tarayya Ruwa a Jallo

Rundunar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Ɗan Majalisar Tarayya Ruwa a Jallo

  • Rundunar 'yan sanda ta ayyana neman ɗan majalisar tarayya na birnin Bauchi, Yakubu Shehu, bisa zargin hannu a aikata muggan laifuka
  • Ta kuma sanya ladan naira miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka da bayanai har aka cafke wanda ake zargin
  • Rundunar ta bayyana manyan laifukan da ake zarginsa da hannu ciki har da tuhumar kisan kai

Bauchi - Rundunar 'yan sanda ta ayyana neman mamban majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Bauchi, Yakubu Shehu, ruwa a jallo.

Channels tv ta rahoto cewa 'yan sanda na neman Yakubu duk inda ya shiga su damƙe shi bisa zargin kisan kai, haɗa baki, illata mutane da kuma gurɓata zaman lafiya.

Yakubu Shehu
Mamba mai wakiltar mazabar Bauchi a majalisar wakilai, Yakubu Shehu Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Wannan ci gaban na ƙunshe ne a wata takarda da aka raɗawa CRO Form 5, wacce ta fito daga Ofishin Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Saura kwanaki zabe, an sace dan takarar majalisar dokokin wata jiha

Rundunar tsaron ta bukaci duk wanda ke da sahihan bayanan inda ɗan majalisar ya shiga ya tuntube ta, kuma ta yi alƙawarin ba da ladan miliyan ɗaya ga duk wanda ya taimaka aka cafke shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Bauchi, Ahmed Wakil ne ya fitar da takarda ta musamman da ta ayyana neman ɗan majalisar ruwa a jallo.

A rahoton The Cable, takardar ta ce:

"Rundunar yan sanda na maraba da duk wanda ke da wasu sahihan bayanai da zasu taimaka a kama shi domin gudanar da bincike daga bisani a gurfanar da shi gaban kuliya."
"Duk wani mai bayanan sirri da zasu taimaka a kama shi ya tuntubi wannan lambar 08151849417 ko kuma ya kai rahoto Caji Ofis mafi kusa."

Yakubu Shehu ya ci zaɓen ɗan majalisar wakilan tarayya karkashin inuwar Peoples Redemption Party (PRP). Ya sauya sheƙa zuwa APC a 2022 daga bisani ya samu tikitin Sanata a jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Ba abinda zai hana mu bacci - PDP

A wani labarin kuma Sakataren PDP Na Jihar Ondo Ya Yi Murabus, Jam'iyyar Ta Yi Martani Mai Zafi

Jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo ta ce ta samu labarin sakaren jiha ya yi murabus amma hakan ba zai girgizata ya hana ta bacci da ido biyu ba.

Rahotanni sun nuna cewa baya ga Sakataren, wasu manyan jiga-jigai sun fice daga PDP a baya-bayan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel