Rundunar Sojin Najeriya Ta Hau Matsayi Na 36 Daga Cikin 145 Mafi Karfin Wuta a Duniya

Rundunar Sojin Najeriya Ta Hau Matsayi Na 36 Daga Cikin 145 Mafi Karfin Wuta a Duniya

  • Najeriya ta koma matsayi na 36 daga cikin jerin kasashe mafi karfin soji 145 a faɗin duniya
  • Haka zalika Najeriya ta sauko daga matsayi na uku zuwa matsayi na hudu a jerin kasashen nahiyar Afirka
  • Ƙasar Amurka ce ta farko a duniya yayin da Masar ke matsayi na farko a nahiyar Afirka kuma tana matsayi na 14 a duniya

Rundunar Sojin Najeriya ta koma matsayi na 36 a duniya yayin da ta koma na Huɗu a nahiyar Afirka, a cewar rahoton global firepower index na baya-bayan nan.

Rundar sojin Najeriya ta yi ƙasa da matsayi ɗaya a jerin rundunar sojoji mafi ƙarfin wuta na duniya da aka bayyana a kwanan nan idan aka yi la'akari da matsayinta a 2022.

Sojojin Najeriya
Rundunar Sojin Najeriya Ta Hau Matsayi Na 36 Daga Cikin 145 Mafi Karfi a Duniya Hoto: Nigerian Military
Asali: UGC

Haka nan Najeriya ta faɗo ƙasa da matsayi ɗaya daga matsayin na uku ta koma na hudu a nahiyar Afirka, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari Na Tsaka Mai Wuya, Ƙungiyar Kwadugu Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Kan Abu 2

Kasashen dake sahun farko a duniya

Rundunar sojin ƙasar Amurka ne na farko a jerin mafi karfi a duniya, sojin ƙasar Rasha na biye mata baya a matsayi na biyu, sai kama China a matsayi na uku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Indiya ta zo na hudu, Burtaniya a matsayi na biyar sai kuma kasashen Koriya ta Kudu, Pakistan, Japan, Faransa da Italiya waɗanda suka zo na shida, Bakwai, Takwas, Tara da 10 a duniya.

Kasashen da ke sahun farko a Afirka

A nahiyar Afirka, kasar Masar ce a matsayi na farko kuma ta 14 a duniya, Algeriya ta zo na biyu kuma ita ce ta 26 a Duniya, Afirka ta Kudu da ke matsayi na 33 a Duniya ce ta zo na uku a faɗin Afirka.

"Ana gane matsayin kowace kasa ne idan aka duba kayan aikin da take da shi. Wannan jerin kasashe mafi karfin soji ya duba muhimman abubuwa kusan 60 kafin gane adadin ƙarfin kowace kasa."

Kara karanta wannan

Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Manyan Ƴan Takarar Gwamnan Jihar Bauchi 2

"Ana duba rukunoni kama daga yawan rassan Soji da karfin arzikin samar da kayan aiki da yanayin ƙasa. A 2023, Najeriya ta fito a matsayi na 36 daga cikin ƙasashe 145 bayan nazari tana da maki 0.5587."

'Yan Boko Haram Sama da 1000 Sun Mika Wuya Bayan ISWAP Ta Kashe 200

A wani labarin kuma Mayakan Boko Haram sama da 1000 sun miƙa wuya ga rundunar sojin Najeriya

An tattaro cewa wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da ISWAP ta hana su rawar gaban hanci, tana farautarsu ta ko ina domin ta kashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel