Ko Dan Maje vs Danbarde: Muhimman Bayanai Game Da ’Yan Takarar Gwamnan APC da PDP a Gombe

Ko Dan Maje vs Danbarde: Muhimman Bayanai Game Da ’Yan Takarar Gwamnan APC da PDP a Gombe

‘Yan Najeriya sun kagu da jiran ranar 18 ga watan Maris domin kada kuri’unsu ga ‘yan takarar gwamnan da suke so su mulki jihohinsu.

A jihar Gombe ma bata sauya zane ba, domin kuwa an samu ‘yan takara biyu masu fada a ji a jam’iyyun siyasa mafi tasiri a Najeriya; PDP da APC.

A wannan rahoton, mun tattara muku bayanan da ya kamata ku sani game da ‘yan takarar gwwamnan biyu; Muhammadu Inuwa Yahaya na APC da Muhammad Jibrin Danbarde na jam’iyyar PDP.

Muhammadu Inuwa Yahaya na jam’iyyar APC

Takaitaccen tarihin Gwamnan jihar Gombe mai ci
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

1. Haihuwarsa

An haifi Muhammadu Inuwa Yahaya a ranar 9 ga watan Oktoban 1961 a jihar Gombe, rahoton The Guardian.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Shiga Neman Tsohon Gwamna Kan ‘Kisan Kai da Garkuwa da Mutane’

Sunan mahaifinsa Alhaji Yahaya Umaru, kuma hamshakin dan kasuwa ne fitacce a jihar Gombe da ketare.

2. Karatunsa

Ya yi makarantar Firamare a Central da ke kwaryar Gombe, kana ya zarce zuwa makarantar sakandaren gwamnati ta kimiyya da ke Jeka da Fari a Gombe.

Hakazalika, ya yi karatun jami’a, inda ya samu digirinsa na farko a ilimin akanta a shekarar 1983 a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

3. Kungiyoyin sana’a da kwarewar ilimi da yake da alaka dasu

Inuwa Yahaya ya kasance daya daga cikin mambobin wadannan kungiyoyin, kuma yana da alaka mai karfi.

  1. Association of Nation Accountants of Nigeria (ANAN),
  2. Nigeria Institute of Management (NIM)
  3. Chartered Institution of Taxation of Nigeria (ACITN)

4. Ahalinsa

Inuwa Yahaya yana da aure; matansa biyu, yana da ‘ya’ya bakwai duk da ke zaune a jihar ta Gombe. A shekarar da ta gabata, 2022 ne dansa babba ya yi aure.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan jihar Arewa ya sha jar miya, 8 cikin 13 na 'yan takarar gwamna sun janye masa

5. Gogewar aiki

Inuwa Yahaya ya yi aiki da gwamnati da kuma cibiyoyi masu zaman kansu. Ya fara aiki ne da gwamnatin jihar Bauchi, a lokacin Gombe na karkashin jihar Bauchi; daga 1984 zuwa 1985.

Ya kasance babban daranta a kamfanin mahaifinsa na A.Y.U mai harkar gine-gine daga 1993 zuwa 1999.

A lokacin mulkin Muammadu Danjuma Goje; 2003, ya samu matsayin kwamishinan kudi da ci gaban tattalin arziki.

6. Rayuwar siyasarsa

Ya shiga harkar siyasa ne a 2003. Ya tsaya takarar gwamna a 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar APC, amma ya sha kaye.

A ranar 1 ga watan Oktoban 2018, ya lashe zaben fidda gwanin gwamnan APC, inda ya samu kuri’u 859, abokin hamayyarsa, Muhammad Jibrin Danbarde ya samu kuri’u 463.

A ranar 9 ga watan Maris 2019 ne aka alanta Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Gombe.

Ya banke Usman Bayero Nafada a zaben, inda ya samu kuri’u 364,179, Bayero ya samu kuri’u 222,868.

Kara karanta wannan

Buni Vs Sherrif: Takaitaccen Bayani Game Da ‘Yan Takarar Gwamnan Jihar Yobe a Zaben Gobe

7. Zaben 2023

A matsayinsa na gwamna mai ci, shine ya lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar a jihar a 2022, kuma yana son komawa a karo na biyu don ci gaba da mulki daga inda zai tsaya.

Muhammadu Jibrin Danbarde na jam’iyyar PDP

Tarihin Muhammad Jibrin Danbarde
Muhammad Jibrin Danbarde, dan takarar gwamnan PDP a Gombe | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

1. Haihuwarsa

An haifi Danbarde a jihar Gombe da ke Arewa maso Gashin Najeriya a shekarar 1972.

2. Karatunsa

Bayan karatun firamare da sakandare, Danbarde ya samu digirinsa na farko a fannin tattalin arziki daga jami’ar Abuja, digiri na biyu a fannin Risk Management daga jami’ar New York da MBA a Imperial College da ke Landan.

Hakazalika, ya yi difiloma a jami’ar Harvard da kuma wani karatun PGD a jami’ar Abubakar Tafawa da ke Bauchi., Daily Trust ta tattaro.

3. Gogewar aiki

Danbarde ne babban jami’in bankin Sun Trust, kuma ya kasance daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar ba da lamuni ta kasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tarihin 'yan takara gwamna biyu na APC da PDP a jihar Arewa mai daukar hankali

Har ila yau, ya yi aiki da Premium Pensions Limited a matsayin darakta da dai sauran manyan ayyuka na gine-gine.

Gabanin kafa bankin Sun Trust, Banbarde ya yi aiki da bankunan Union, Citygroup N.A da kuma Barclays, rahoton Daily Trust.

4. Rayuwar siyasarsa

A shekarar 2019, ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar APC, inda ya fadi a zaben fidda gwani aka ba Inuwa Yahaya, gwamnan Gombe mai ci a yanzu.

Daga baya ya koma jam’iyyar PDP, inda ya sake tsaya takarar gwamna a wannan shekarar ta 2023.

5. Zaben 2023

A zaben 2023, dan takarar gwamnan na PDP na da burin kwace kujerar gwamna mai ci, Muhammadu Inuwa Yahaya.

A ranar 18 ga watan Maris ne dai za a yi zaben, kuma dukkan ‘yan takarar jam’iyyun siyasar a shirye suke don cimma burinsu.

-

Asali: Legit.ng

Online view pixel