Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Wasu Shaguna a Kasuwar Rimi Ta Kano da Wasu Kauyukan Jigawa Uku

Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Wasu Shaguna a Kasuwar Rimi Ta Kano da Wasu Kauyukan Jigawa Uku

  • An samu aukuwar wata mummunar gobara da ta tashi hankalin jama’ar kauyuka uku a jihar Jigawa da ke makwabtaka da jihar Kano
  • An bayyana yadda mataimakin gwamna ya zo wurin da gobarar ta faru, inda aka yi nasarar kashe ta wutar ba tare da bata lokaci ba
  • Hakazalika, an yi irin wananan gobarar a wata kasuwa shahararriya a jihar Kano, inda shaguna kusan 21 suka kone kurmus

Arewa maso Yamma - Wasu kauyuka uku a karamar hukumar Kiyawa a jihar Jigawa sun kama da wuta, kamar yadda rahoton kafar labarai ta Channels ya bayyana.

Gobarar ta cinye gidaje, dabbobi, amfanin gona da sauran kayayyaki masu da daraja a Malamawar Dangoli, Karangi da kuma Kwalele a karamar hukumar ta Kiyawa.

Wani ganau da ya ga yadda gobarar ta kama ya bayyana cewa, hakan ya faru ne sakamakon yadda iska ta dauko tartsatsin wuta daga murhu, inda ta kama gidan kara da ke yankunan.

Kara karanta wannan

Toh fa: An sanyawa masallaci sunan gwamna Kirista, kungiyar Musulmai ta yi martani

Gobara ta yi barna a jihohin Kano da Jigawa
Yadda gobara ta lamushe shaguna da kauyuka uku a Jigawa da Kano | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wata gobara ta cinye shaguna masu yawa a kasuwar Rimi ta Kano

Lamari irin wannan ya faru a kasuwar Rimi da ke jihar Kano mai makwabtaka ta kut-da-kut da jihar ta Jigawa a Arewa maso Yammacin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa, gobarar ta Kano ta yi sanadiyyar konewar shaguna har 21 nan take.

An samu wutar ta lafa yayin da daga baya kuma babban daraktan hukumar ba da agajin gaggauta ta kasa (NEMA), Mustapha Habib da kuma mataimakin gwamna suka ziyarci kauyukan na Jigawa.

Gobara ta ama ruwan dare a Najeriya

Barkewar gobara a kasuwannin Najeriya ya fara zama ruwan dare a wannan lokacin, kuma rashin samun daukar matakin gaggawa na sa a yi asarar manyan dukiyoyi da ma asarar rayuka.

A lokuta mabambanta a Najeriya, an sha samun gobara a kasuwanni, inda ‘yan kasuwa ke tafka asarar miliyoyin kudade.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya: Kwankwaso Ya Karbi Bakuncin Mutum 17 Da Suka Samu Nasara a Zaben Majalisa

Mafi akasarin tashin gobarar na farawa ne daga turken wutar lantarki da ake amfani da ita a bangarori daban-daban na kasuwannin.

Yadda gobara ta lamushe kasuwar jihar Borno

A wani labarin, kunji yadda wata gobara ta tashi a babban kasuwar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya a ranar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.

Wannan lamarin ya tada hankali, domin kuwa ya kawo mummunan asara ga ‘yan kasuwan da ke neman halaliyarsu a shahararriyar kasuwar.

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana aniyar tallafawa ‘yan kasuwan da makudan kudade domin samun damar warwarewa da kuma rage asarar da ta shafe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel