Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Maiduguri Ta Jihar Borno

Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Maiduguri Ta Jihar Borno

  • Mummunar gobara ta tashi a shahararriyar kasuwar nan ta 'Monday Market' da ke garin Maiduguri a jihar Borno
  • Dubban shaguna sun kone kurmus a gobarar inda aka yi asarar dukiya ta miliyoyin naira
  • Hukumar kashe gobara ta kwana-kwana na nan tana kokarin kashe wutar wacce ba a san musababbin tashinta ba

Borno - Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa gobara ta tashi a babbar kasuwa ta 'Monday Market' da ke jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta fara da misalin karfe 2:00 na tsakar daren ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairu kuma ta yadu zuwa bangarori daban-daban na kasuwar.

Kasuwar da gobata ta tashi a Maiduguri
Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Maiduguri Ta Jihar Borno Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, ba a san musababbin abun da ya haddasa gobarar ba kuma jami'an kwana-kwana na nan suna kokarin kashe wutan.

Kara karanta wannan

Tambuwal Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Karbi Sakamakon Zaben 2023

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gobarar ta lakume daruruwan shaguna yayin da aka yi asarar dukiya na miliyoyin naira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani bidiyo da jaridar Aminiya ta wallafa a shafinta na Twitter, an gano motocin hukumar kashe gobara da dama a kasa suna ta kokarin ganin sun kashe gobarar da ke ta ci a cikin kasuwar.

Hukumar kashe gobara ta yi martani

Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Umaru Kirawa ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labaran NMajeriya, yana mai cewa sashin kwana-kwana na jihar da na tarayya daga bangarori daban-daban sun yi hadaka don dakile annobar.

“Mun dauki cikakken matakai don daidaita lamarin,” inji Kirawa.

Kada ku kashe ne zan fallasa sirrin da ke boye, wata matashiya ta zauce

A wani labari na daban, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon wata budurwa da ta zaune yayin da wasu yan boye ke bibiyarta tare da yi mata barazana da ranta.

Kara karanta wannan

Jajiberin zabe: Tashin hankali yayin da aka dasa bam a gidan dan takarar majalisa na APC

Kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an jiyo matashiyar tana sambatu tare da neman agaji cewa wasu na bibiyarta kuma suna yi mata barazana saboda wani sirri na boye.

Har ma tana ikirarin cewa za ta tona sirrin da ta binne amma dai kada a barsu su hallaka ta lamarin da ya sa wasu da dama tausaya mata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel