Yan Bindiga Sun Sake Shiga Abuja, Sun Garkuwa da Mutane Tara

Yan Bindiga Sun Sake Shiga Abuja, Sun Garkuwa da Mutane Tara

  • Yan bindiga sun kai sabon hari kan wani rukunin gidaje a Abuja, sun sace mutane akalla 9
  • Wani mazaunin yankin ya ce lamarin wanda ya faru da karfe 11:30 na dare ya haddasa tashin hankali
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Abuja ta ce dakaru sun baza komarsu a dajin yankin

Abuja - Akalla mutane 9 ne wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba da su a rukunin gidajen Grow Homes Estate da ke gefen Kuchibiyi, yankin Kubuwa a birnin tarayya Abuja.

Jaridar Punch ta tattaro cewa 'yan bindigan da suka kai adadin mutane 20 sun kutsa rukunin gidajen da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Jumu'a, suka aikata ɗanyen aikin.

Harin yan bindiga.
Yan Bindiga Sun Sake Shiga Abuja, Sun Garkuwa da Mutane Tara Hoto: punchng
Asali: UGC

Wani mazaunin Anguwar mai suna Hassan a takaice, ya ce maharan sun dauki mutane 9 a gidaje biyu da ke cikin rukunin Anguwar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Ta'adda Suka Tafi Har Gida Suka Kashe Ɗan Malamin Addini, Sace Matarsa A Kaduna

Mutumin ya kara da cewa harin 'yan bindigan ya jefa mazauna yankin cikin yanayin fargaba da tashin hankali. A kalamansa ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jiya da misalin karfe 11:30 wasu 'yan bindiga da yawa suka kai hari rukunin gidajen Grow homes estate, kusa da Kuchibiyi. Mun ji ƙarar harbin bindiga, mun shiga tashin hankali."
"Da muka je wurin da safiyar nan mun gano maharan sun kai mutane 20, sun shiga gida gida suna kwace wa mutane kayayyakinsu. Sun tafi da aƙalla mutane 9, har da mata da kananan yara."
"Sun gudu ta cikin jeji wanda yake ɓulla kauyen Paze. 'Yan sanda da jami'an tsaron rukunin gidajen sun bazama bincike a cikin jejin tun safe domin ceto waɗanda aka sace."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntube ta, jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da lamarin, ta ce dakaru da masu gadin wurin sun mamaye dajin wurin don ceto mutanen.

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Sahara Reporters ta rahoto kakakin 'yan sandan na cewa:

"Muna samun labari muka tura dakaru wurin, da ganin jami'ai maharan suka ari na kare kuma suka ɗauki wasu mazauna suka yi cikin jeji."
"Har kawo yanzu jami'an 'yan sanda da masu gadin anguwar na cikin Daji domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su lami lafiya."

Kakakin yan sanda ta roki mazauna Anguwar su kwantar da hankulansu kana su taimaka wa 'yan sanda da sahihan bayanai domin kame maharan.

A wani labarin kuma Yaro Ya Bindige Abokiyar Wasarsa Yar Shekara 3 Har Lahira A Ogun

Rahotanni sun bayyana cewa yaron ɗan kimanin shekara 13 a duniya ya zare bindiga ya halaka karamar yarinyar yayin da suke tsaka da wasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel