Yadda Sojoji Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda Da ’Yan Daban Siyasa da Ke Shirin Kawo Cikas Ga Zabe

Yadda Sojoji Suka Fatattaki ’Yan Ta’adda Da ’Yan Daban Siyasa da Ke Shirin Kawo Cikas Ga Zabe

  • Hukumar tsaro a Najeriya ta bayyana yadda ta kame ‘yan ta’adda da yawa a jihar Kogi a ranar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu
  • Hakazalika, sun fatattaki wasu ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas bayan gano suna shirin kitsa tsaiko ga zaben bana
  • A ranar 18 ga watan Maris ne za a yi zaben gwamnoni a Najeriya, ana ci gaba da shiri tsakanin jami’an tsaro, ‘yan kasa da ‘yan siyasa

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta Najeriya (DHQ) ta ce jami’anta da ke aiki a Arewacin Najeriya sun yi nasarar dakile hare-haren kawo tsaiko ga zaben 2023, TheCable ta ruwaito.

Wannan na fitowa ne daga bakin daraktan yada labarai na hukumar, Musa Danmadami, inda yace ‘yan ta’adda ne suka kitsa hare-haren da ka iya zama matsala ga zaben na bana.

Kara karanta wannan

An shuka dusa: Jama'a sun koka, 'yan siyasa sun karbi lambar asusun bankinsu a zaben shugaban kasa

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, ya ce a jajibirin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, jami’an sun samu labarin shirin tsageru a Kauwa, Gobaru da Munguno a jihar Borno.

Yadda sojin Najeriya suka fatattaki 'yan daba a Borno da Kogi
Sojin Najeriya kenan a bakin aiki | Hoto: thedefensepost.com
Asali: UGC

Musa Damadami ya bayyana cewa, bayan samun bayanan sirri, jami’an sojin sama sun yi nasarar gano maboyar ‘yan ta’addan tare da lalata komai da suka mallaka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An kama ‘yan daban siyasa a Kogi a ranar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu

Ya kara da cewa, jami’an sun kuma yi nasarar kwamushe mutane takwas da ake zargin ‘yan daban siyasa ne a ranar zabe a yankin Okehi da ke karamar hukumar Okenne a jihar Kogi.

Daraktan na yada labarai ya ce, an kama ‘yan daban ne a lokacin da suke kokarin lalata shirin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a yankin, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Ana dab zabe, gwamnan Arewa sabon nadi, ya nada Dije Aboki a ma'aikatar shari'a

Hakazalika, ya ce an kwato makamai da suka hada da bindigogi uku masu tashi, AK47 hadin gida guda biyu, bindigogi kirar gida guda shida da kuma adduna masu kaifi guda biyu daga ‘yan daban siyasan.

Hukumar INEC har ta fara raba kayan aikin zabe

A wani labarin kuma, kun ji yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fara rarraba kayan aikin zabe a jihar Kaduna.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba, kafin daga bisani hukumar ta bayyana dage zaben gwamnoni na ranar 11 ga watan Maris zuwa 18 ga watan.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da shirin yin zaben gwamnan da aka shafe shekaru hudu ana jira a wasu jihohi daga cikin 36 na Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel