Idan Aka Zabe Ni, Zan Fara Ba Matasan Delta N30,000 Duk Wata, Inji Dan Takarar Gwamna Na SDP

Idan Aka Zabe Ni, Zan Fara Ba Matasan Delta N30,000 Duk Wata, Inji Dan Takarar Gwamna Na SDP

  • Dan takarar gwamnan SDP a jihar Delta ya bayyana kadan daga alheran da ya shirya yiwa ‘yan jiharsa idan aka zabe shi
  • A cewarsa, zai habaka tattalin arzikin jihar tare da farfado da masana’antar atamfa ta Asaba da ba ta aiki a yanzu
  • Ya kuma yiwa matasa alkawarin ba su N30,000 duk wata idan ya samu damar hawa kujerar gwamna a jihar

Asaba, jihar Delta - Dan takarar gwamna a jam’iyyar SDP a jihar Delta, Cif Kenneth Gbagi ya yi alkawarin farfado da masana’antar atamfa ta Asaba idan aka zabe shi a ranar Asabar mai zuwa, Punch ta ruwaito.

Gbagi ya bayyana hakan ne a taron kamfen dinsa da ya samu halartar manyan fastoci daga coci daban-daban na jihar a birnin Asaba a jiya Asabar 4 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Ku taimake ni: Gwamnan PDP ya yi murya kasa-kasa, ya roki mata alfarma a zaben ranar Asabar

Ya bayyana cewa, a shekararsa ta farko a kn karagar mulki, zai tabbatar da farfado da masana’antar atamfa ta Asaba.

Dan takarar gwamna ya yi alkawarin kawo sauyi a jihar Delta
Cif Kenneth Gbagi kenan, dan takarar gwamna | Hoto: withinnigeria.com
Asali: UGC

A cewarsa, ta haka ne zai samar da hanyar fitar kayayyakin da aka sarrafa a kasa Najeriya zuwa wasu kasashen waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zan habaka tattalin arzikin Delta

Ya kuma bayyana cewa, hakan zai habaka tattalin arzikin jihar tare da fadada hanyoyin kudaden shiga ga jihar.

A bangare guda, ya ce masana’antar za ta kawo ayyukan yi ga matasa, inda ya kara da cewa, makarantun gwamnati a jihar za su kasance kyauta daga firamare har sakandare.

Ya kuma koka da halin da makarantun gwamnati suke ciki a jihar, inda yace hakan ba abu ne da ya kamata ya ci gaba da faruwa ba.

Zan fara ba matasa N30,000 duk wata

A jawabinsa, ya kara da cewa, daga ranar 1 ga watan Yunin 2023 idan aka zabe shi, zai fara ba matasan Delta N30,000 a kowane wata, Within Nigeria ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: Aiki ya kankama, an yi mota mai amfani da ruwa a jami'ar Arewacin Najeriya

Ya kuma yi alkawarin ilmantar da masa sanin na’ura mai kwakwalwa, kuma zai tabbatar da samo rumbun bayanansu na musamman.

A bayanin nasa, ya kuma gargadi matasa da kada su bari wani ya yaudare su da alkawuran karya, inda yace shi yake da mafita ga matsalolin Delta.

Daga karshe ya yiwa kansa addu’ar cewa, idan aka zabe shi kuma ya yi abin da sauran ‘yan siyasa ke yiwa jama’a, to kada Allah ya barshi lafiya.

An kuma yada jita-jitan cewa, wani gwamnan APC ya ce zai ba duk wanda ya zabe shi N20,000 a zaben bana na ranar 11 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel