Na Shawarci Peter Obi Ya Janye Daga Takara, Amma Ya Yi Kunnen Kashi, Inji Tsohon Gwamnan Anambra, Arthur Eze

Na Shawarci Peter Obi Ya Janye Daga Takara, Amma Ya Yi Kunnen Kashi, Inji Tsohon Gwamnan Anambra, Arthur Eze

  • Tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana kadan daga abin da ya tattauna da dan takarar shugaban kasa na Labour a baya
  • A cewar Price Arthur Eze, babu yadda za a yi ace Peter Obi ya zama shugaban kasan Najeriya a yanzu
  • Ya shawarci Peter ya janye daga takara, amma ya yi kunnen kasa tare da bayyana masa jihohin da zai iya lashe zabe

Jihar Anambra - Tsohon gwamnan jihar Anambra da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour sun shiga kanun labarai a cikin kwanakin nan.

Batu ne da ke da alaka da yaba ma Peter Obi, goyon bayansa ko kushe shi, ko ma dai sukarsa game da aniyarsa da don mulkin Najeriya.

Peter Obi dai ya sha bayyana cewa, zai fitar da Najeriya daga jerin kasashe masu yawan sayen kayan waje zuwa mai samar da kayayyaki da kanta.

Kara karanta wannan

Bana son rigima: Buhari ya fadi abu 1 da zai yi bayan sauka daga mulki a 2023

Tsohon gwamnan Anambra ya ce Peter Obi ba zai ci zabe ba
Na Shawarci Peter Obi Ya Janye Daga Takara, Amma Ya Yi Kunnen Kashi, Inji Tsohon Gwamnan Anambra, Arthur Eze | Hoto: anambrapeople.com.ng
Asali: UGC

A jiya Litinin 26 ga watan Disamba, attajirin da jihar Anambra, Price Arthur Eze ya yi fatali da aniyar Peter Obi ta gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 202, rahoton Vanguard.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Eze, yayin da yake magana a wani taron gargajiya na Ofala a masarautar mai martaba Igwe (Dr.) Robert Eze na Ukpo a karamar hukumar Dunukofia a jihar ya ce ya gargadi Obi kan batun tsayawa takara, amma ya yi kunnen kashi.

Ya ankarar da Peter Obi, amma ya ki daukar shawara ta, inji Eze

Ya bayyana cewa, ya shawarci Obi kan ya jira wani lokaci, amma ya ki sauraransa, kawai ya kirgo masa jihohin da yake kyautata zaton zai ci zabe, Tribune Online ta ruwaito.

A kalamansa:

“Na gargadi Peter Obi kan ya janye daga takarar amma ya yi kunnen kashi. Na fada masa karara cewa, babu ruwana da shirinsa. Na fada masa ya yi nesa da wannan muradin, ya jira nan gaba.

Kara karanta wannan

PDP A Kano: Aminu Wali Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Bayan Kotu Ta Ba Wa Abacha Nasara

“Lokacin da ya fada min muradinsa, na tambaye shi jihohin da yake tunanin zai ci zabe a yankunan Yamma da kuma Arewa – ya fada min; amma ban gamsu ba. Na fada masa ba zai ci zabe ba; don haka kada ya bata lokacinsa da kudinsa.”

A bangare guda, Peter Obi ya gaba da Goodluck Jonathan; tsohon shugaban kasa a Najeriya kan batun takararsa, ya ba shi shawari kan abin da ya kamata zai yi idan ya gaji Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel