Yabon Tinubu: Shin Fayose Ya Fita Daga Jam'iyyar PDP, Gaskiya Ta Fito Filli

Yabon Tinubu: Shin Fayose Ya Fita Daga Jam'iyyar PDP, Gaskiya Ta Fito Filli

  • Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti ya karyata cewa ya fita daga jam'iyyarsa ta PDP, amma ya ce yana girmama Bola Tinubu
  • Fayose, ya yi karin haske yana mai cewa ya koma gefe guda ne, don ya samu damar yin wasu maganganu ga shugabanni
  • Tsohon shugaban kungiyar gwamnonin na PDP ya nanata cewa ko da zai bar PDP ba zai taba shiga APC ba

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a ranar Juma'a, ya karyata rahoton cewa ya yi murabus daga jam'iyyar PDP bayan kayen da jam'iyyar ta sha a zaben shugaban kasa na ranar Asabar.

Fayose, wanda ya jadada cewa shi dan jam'iyyar PDP ne, ya ce ba murabus ya yi ba kawai dai ya janye ya koma gefe guda ne, rahoton The Punch.

Ayo Fayose
Ayo Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: An gano sunayen makiyaya 37 da jirgin sojin sama ya babbaka a jihar Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohon gwamnan, cikin sanarwa da ya rattaba hannu da kansa mai taken "Ban yi murabus daga PDP ba, na koma gefe ne - Ayo Fayose," ya bukaci yan Najeriya su cigaba da goyon bayan PDP musamman a zaben gwamna da majalisa.

Sanarwar ta Fayose ta ce:

"Har yanzu ni dan jam'iyyar PDP ne. Na dan koma gefe ne saboda in fada wa masu mulki gaskiya ba tare da ana yi wa kallon magana ta da jam'iyya ba. Akwai hanyar yin murabus daga jam'iyyar siyasa kuma zan bi hanyoyin idan bukatar ta tashi.
"Yana da kyau mu samu wanda zai iya fadan gaskiya ba tare da alakanta kansa da jam'iyya ba.
"Ni mamban PDP ne, ni mamban kwamitin shugabanni na PDP na kasa ne, mamba na kwamitin amintattu kuma a matsayi na na tsohon shugaban kungiyoyin gwamnonin PDP. Mamba ne na dindindin. Amma Najeriya ta fi kowanne jam'iyya girma."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Tsageru Sun Yanka Jagoran APC Har Lahira Bayan Tinubu Ya Ci Zabe

Ni ba dan jam'iyyar APC bane, Fayose

Fayose ya kuma yi karin haske cewa shi ba dan jam'iyyar APC bane kuma ba zai taba shiga wata jam'iyyar ba, ya kara da cewa, amma, yana matukar girmama Tinubu.

Ya kuma ce yana da ikon zaben ra'ayinsa kan menene adalci a zaben shugaban kasar na 2023.

Har wa yau ya ce baya sha'awar yin takarar wata kujerar siyasa a rayuwarsa, yana mai cewa:

"Takara mai zan yi ina shekaru 62? Ko da zan yi takara, ba a APC ba, na sha nanata wa ba zan taba shiga jam'iyyar APC ba kuma har yanzu ina fada."

Asali: Legit.ng

Online view pixel