An Bayyana Sunayen Makiyayan da Sojin Najeriya Suka Kashe a Farmakin Jirgin Sama a Nasarawa

An Bayyana Sunayen Makiyayan da Sojin Najeriya Suka Kashe a Farmakin Jirgin Sama a Nasarawa

  • Bayanan mutanen da suka mutu a wani farmakin soji ya bayyana, an ce mutum 37 ne suka rasa rayukansu nan take
  • Rahoto ya bayyana cewa, sojoji sun yi luguden wuta kan wasu makiyaya da suke tare da shanunsu a jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya
  • Ya zuwa yanzu, kungiyar Fulani ta ce ba a samu gwamnatin da ta jajanta ko daukar mataki kan lamarin da ya faru ba

Jihar Nasarawa - Bayan mutum 37 da jirgin sojin saman Najeriya ya kashe a garin Akwanaja na karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa ya bayyana.

A baya kun ji cewa, makiyaya 37 ne farmakin jirgin saman sojin Najeriya ya kashe a ranar 24 ga watan Janairun bana.

Daily Trust ta ruwaito cewa, makiyayan suna hanyarsu ta dawowa daga Makurdi ta jihar Benue ne, inda suka karbo shanayensu 1000 da gwamnati ta kwace.

Kara karanta wannan

"Yanzu Yan Boko Haram Sun Koma Sanya Tufafin Mata Yayin Kai Hare-Hare" - Inji Ndume

Yadda aka kashe wadanda basu ji ba basu gani ba a Nasarawa
Taswirar Nasarawa, jihar da aka farmaki makiyaya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu, hukumar tsaro, soji ko gwamnatin Najeriya babu wanda ya bayyana bayani ko batu mai daukar hankali game da wannan kisa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Sule ya yi magana, soji sun yi magana

Sai dai, a wani taron manema labarai, daraktan yada labarai na gidan soji, Manjo Janar Musa Danmadami ya shaida cewa, ba zai yi magana game da batun ba tunda gwamna Abdullahi Sule ya yi.

A cikin wani jerin sunaye da Daily Trust tace ta samo a ranar Alhamis 2 ga watan Maris, 2023, an gano gawarwakin mutum 31 kuma har an yi musu jana’iza, yayin da shida kuwa suka kone kurmus.

An samu jerin sunayen wani koke da kungiyar ci gaban Fulani ta FGDRI ta aikewa hukumar kare hakkin dan Najeriya dauke da sa hannun shugabanta, Salim Musa Umar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yan Daba Sun Tafi Gidan Wani Dan Gani Kashe Nin Tinubu, Sun Lakada Wa Mahaifiyarsa Duka, Sun Kona Motarsa

Umar ya bayyana cewa, an jikkata mutum tara a farmakin, kuma har yanzu suna ci gaba da karbar kulawar asibiti a asibitin kwararru da ke Lafia a Nasarawa.

Ya kuma shaida cewa, wasu daga cikin jami’an sojin sun bi dangin kadan daga dangin wadanda lamarin ya rutsa dasu don kulle musu baki kan abin da ya faru.

Jerin wadanda lamarin ya rutsa dasu

1. Abubkar Haruna (Namiji)

2. Jibirin Alh. Ja’oji (Namiji)

3. Ibrahim Alh. Ardo (Namiji)

4. Jammini Haruna (Namiji)

5. Audu Haruna (Namiji)

6. Abdulkarim Haruna (Namiji)

7. Yusuf Haruna (Namiji)

8. Okki Haruna (Namiji)

9. Chelowa Haruna (Namiji)

10. Alh. Diyam Haruna (Namiji)

11. Dambo Alh. Diyam (Namiji)

12. Jammini AlhDiyam (Namiji)

13. Mohammad Sale (Namiji)

14. Alh. Muhammad (Namiji)

15. Alh. Abubakar (Namiji)

16. Hassan Alawa (Namiji)

17. Muhammad Abubakar (Namiji)

18. Alh. Adamu Baso (Namiji)

19. Ibrahim Moh’d (Namiji)

20. Ibrahim Yakubu (Namiji)

21. Moh’d Dari (Namiji)

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba sun sa wuta a hedkwatar hukumar INEC a wata jihar Arewa

24.Cheers Alh. Oli (Namiji)

25.Pagilo Madugu (Namiji)

26.Tata Huyajo (Namiji)

27.Soja Bawa (Namiji)

28.Abubakar Jibir (Namiji)

29.27.Dando Malam Mama (Namiji)

30.Abubakar Kowa (Namiji)

31.Amadu Husaini (Namiji)

32. Wani direba da ba bayyana sunansa ba (Namiji)

33. Wani mahauci da ba a bayyana sunansa ba (Namiji)

Asali: Legit.ng

Online view pixel