Daga Gama Zabe, An Yi Wa Jagoran APC Yankar Rago a Jihar Osun

Daga Gama Zabe, An Yi Wa Jagoran APC Yankar Rago a Jihar Osun

  • Yayin da Bola Ahmed Tinubu da magoya bayansa ke murnar samun nasara, an je har gida an yanka jagoran APC a jihar Osun
  • Shugaban APC na jiha, Tajudeen Lawal, ya zargi yan daban PDP da kitsa harin wanda ya yi ajalin jigon siyasar jiya Laraba
  • Kakakin hukumar yan sanda ya ce tuni jami'ai suka fara bincike don gano asalin abinda ya faru har ta kai ga kisan kai

Osun - 'Yan daban siyasa sun halaka wani jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a garin Ijesa da ke jihar Osun, Mista Tunde Ejoka, da safiyar jiya Laraba.

The Nation ta tattaro cewa an kashe Ejoka ne a gidansa da ke garin Ijebu-Jesa, hedkwatar karamar hukumar Ori-Ade a jihar Osun, kudu maso yamma.

Tambarin APC
Jam'iyyar APC mai alamar tsintsiya. Hoto: APC
Asali: Instagram

Shugaban APC na rikon kwarya a jihar, Tajudeen Lawal, ya bayyana kisan da babban abun takaici da Allah wadai a wata sanarwa ta ya fitar.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Haka nan ya yi zargin cewa yan daban siyasa da ke goyon bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne suka kitsa tare da aikata wannan ɗanyen aikin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lawal ya kara da cewa dama 'yan daban PDP sun yi wa marigayi Ejoka barazana yayin da ake tsaka da kaɗa kuri'u ranar zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya.

Ya ce:

"Yankar rago aka yi wa Ejoka, laifinsa kawai na tattara wa jam'iyyarsa ta APC kuri'u masu yawa a karshen makon nan."

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya ce, "A halin yanzu muna kan bincike don gano yanayin abun da har ta kai ga kisan kai."

Haka zalika mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Bamiji Oladele, bai ɗaga kiran salular da aka masa ba yayin da aka tuntuɓe shi don jin ta bakinsa.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito, An Bayyana Gwamnan PDP Da Ya Taimaka Aka Kayar da Atiku Ranar Zabe

A wani labarin kuma Dan takarar LP, Peter Obi ya sha alwashin kalubalantar nasarar Bola Tinubi a Kotu

Obi, tsohon gwamnan Anambra, ya zo na uku a bayan zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Sai dai duk da miliyoyin kuri'un da Tinubu ya tsere masa da su, Obi ya ce karfa-karfa aka masa amma shi ne ya lashe zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel