Rudani Yayin da Aka Tsinci Gawar Mace da Yaro Karami a Cikin Wani Gida a jihar Kano

Rudani Yayin da Aka Tsinci Gawar Mace da Yaro Karami a Cikin Wani Gida a jihar Kano

  • Allah ya yiwa wata mata rasuwa tare da danta a cikin wani gida a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Majiya ta bayyana cewa, an yi kwanaki kusan hudu kafin daga bisani aka ji alamar mutuwarta a cikin daki
  • Ya zuwa yanzu, an tattara gawarwakin zuwa asibiti don ci gaba da bincike, kamar yadda rahoto ya bayyana

Jihar Kano - An tsince gawar wata mata mai suna Aisha Ishaq da danta mai watanni shida a duniya a cikin dakinta a gidan aurenta da ke ‘Yan Awaki a Unguwa ta karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano.

City & Crime ta tattaro cewa, an gano gawarwakin ne kwanaki uku bayan da aka daina ganin matar a unguwar.

Shugaban yankin, Alhaji Ali Abdullahi Usman ya ce matar, wacce mijinta direban tanka ne ta rasu ne a ranar Asabar amma mutane basu gane hakan ba sai ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: An gano sunayen makiyaya 37 da jirgin sojin sama ya babbaka a jihar Arewa

Yadda aka tsinci gawar wata mata da danta a Kano
Taswirar jihar Kano a Arewa maso Yamma | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Yadda aka gani ta rasu

A cewarsa, makwabta sun gano akwai matsala ne bayan da suka shafe kwanaki kusan hudu basu ganta ba, sai kuma suka ji wari na fita daga cikin gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Lokacin da suka sanar dani, na tafi na shaidawa yan sanda. Mun haura gidan da tsani. Bayan fashe kofar, mun same ta da danta a mace a cikin gidan sauro a kan gado. Tuni har ta rube.
“Game da danta, duk da shima ya mutu amma gawarsa bata rube ba. Kamar ya rasu ne washegari ko dai makamancin haka. Ana kyautata zaton yunwa ce ta kashe shi saboda mahaifiyarsa ta mutu kuma babu abin da zai ci.”

An tattara gawarwakin zuwa asibiti

Ya kara da cewa, sun dauki gawarwakin zuwa asibiti tare da rakiyar jami’an ‘yan sanda, Within Nigeria ta tattaro.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yan Daba Sun Tafi Gidan Wani Dan Gani Kashe Nin Tinubu, Sun Lakada Wa Mahaifiyarsa Duka, Sun Kona Motarsa

Shi ma da yake magana, makwabcin marigayiyar, Abubakar Muhammad ya ce:

“Matar ba ta da lafiya. Mijinta, Abubakar Muhammad ya ga kamar ciwo ne karami don haka ya yi tafiya. Mutane sun san da rashin lafiyarta amma sam tunani bai zo kan a duba gidan ba.”

Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan mutuwa mai ban tsoro ba, an yi irin haka a jihar Bauchi, inda aka tsinci gawar mace da namiji a cikin daki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel