'Yan Sanda Sun Gano Wasu Rubabbun Gawarwaki 2 a Jihar Bauchi

'Yan Sanda Sun Gano Wasu Rubabbun Gawarwaki 2 a Jihar Bauchi

  • 'Yan sanda a jihar Bauchi sun bankado wasu gawarwaki biyu da aka gano a wani daki a Rafin Tambari
  • Tuni aka dauki gawarwakin da suka hada mace daya da namiji da ake tunanin sun mutu ne tare a dakin
  • Ya zuwa yanzu dai ba a san sanadi ba, amma ana ci gaba da bincike don gano abin da ya faru

Jihar Bauhci - Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ya bankado wasu gawarwakin mutane biyu da suka mutu a wani daki a kwaryar jihar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Ahmad Wakil ne ya bayyana hakan a Bauchi, inda yace an gano gawarwakin ne a ranar Litinin a wani daki da ke Rafin Tambari a jihar.

Ya kuma bayyana cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar, Alhassan Aminu ya ba da umarnin zurfafa bincike don gano musabbanin mutuwarsu, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Zamfara sun tona moboyar su Turji yayin da sojoji ke neman 'yan ta'adda ruwa a jallo

An gano wasu gawarwaki a wani daki a Bauchi
'Yan Sanda Sun Gano Wasu Rubabbun Gawarwaki 2 a Jihar Bauchi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yadda aka gano inda gawarwakin suke

Wakil ya ce, wani mutum dan unguwar GRA a jihar ne ya shigar da batun batan mai gidansa mai suna Dele Benjamin da ke zaune a Rafin Tambari ga ofishin yanki na 'yan sanda.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wakil ya mutumin ya kwana biyu bai ga mai gidansa ba, sai ya tafi nemansa a gida.

A cewarsa:

"Ya tafi zuwa gidansa a Rafin Tambari don duba shi amma ya tarar gidan a rufe ta ciki.
"Ya buga kofa amma babu wanda ya amsa. Daga nan ya tsallaka ta katanga inda ya fara jin wani wari mara dadi amma bai iya shiga dakin ba."

Ya ce daga nan ya kai rahoto ga ofishin yanki kuma aka tura jami'ai bisa umarnin kwamishinan 'yan sanda domin ganewa idonsu abin da ya faru da kuma kokarin dauko gawarwakin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shigar Ango Wurin Shagalin Aurensa a Akwatin Gawa Ya Gigita Amarya

Ya kara da cewa, yayin da jami'ai suka isa gida, sai suka ji tsananin wari da ke fitowa daga ciki.

A cewarsa, an yi nasarar bude gidan da taimakon da jama'a suka bayar, People Gazette ta tattaro.

Ya ce an kuma tsinci wata gawar wata mace da ba a gano wacece ba a gefen Dele.

Tuni aka dauki gawarwakin zuwa asibiti domin ci gaba da bincike yadda ya dace.

Uba ya mutu a hannun agolansa garin gwada maganin bindiga a Adamawa

A wani labarin, wani mutum ya ba agolansa bindiga ya gwada a kansa bayan da ya karbi maganin bindiga a hannun wani.

An samu bacin rana, uban ya mutu nan take da dan dirka masa alburushin bindiga.

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta shiga lamarin, ya bayyana yadda abin ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel