"Ba A Taba Yin Ingantaccen Zabe Na Gaskiya Kamar Na 2023 Ba A Najeriya", Kashim Shettima

"Ba A Taba Yin Ingantaccen Zabe Na Gaskiya Kamar Na 2023 Ba A Najeriya", Kashim Shettima

  • Zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana zaben 2023 a matsayin zabe mafi inganci a tarihin Najeriya
  • Shettima ya bayyana haka yayin da ya ke zantawa da BBC Hausa ranar Laraba, jim kadan bayan bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe
  • Kashim ya bukaci abokan adawa da su hada kai don yin aiki tare kuma su karbi faduwa ko don cigaban kasarmu

Sanata Kashim Shettima, zababben mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya ce zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 shine mafi gaskiya, inganci, adalci da kuma tsari a tarihin Najeriya a fahimtarsa.

Shettima, a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC, ya bukaci yan yan jam'iyyar adawa da su yadda da faduwa saboda cigaban kasar.

Kashim Shettima
Ba a taba ingantancen zabe irin na ranar 25 ga watan Janairun 2023 ba a tarihin Najeriya, in ji Shettima. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Ta tabbata: INEC ta ba Tinubu da Shettima shaidar su suka lashe zaben shugaban kasa

Ya ce:

''A iya sani na, zaben ranar Asabar shine mafi gaskiya, adalci da kuma tsari da aka taba gudanarwa a Najeriya. An gudanar da zabe cikin tsari kuma masu kira da a soke zabe sun kasa kawo hujjar inda aka samu matsala.
''Dan takarar mu Bola Tinubu ya fadi a jihar sa, ba muyi korafi na. Tun 2003 Buhari bai taba faduwa a jihar Katsina ba amma bana ya fadi, ba muyi korafi ba, me su ke so mu ce?
''A Abia, mun samu kuri'a 8,914 yayin da dan takarar LP ya samu 327,995, ba mu yi korafi ba, mun yadda da sakamakon a yadda yazo. Jam'iyyar LP ce ta lashe Abuja, Nasarawa da Filato, a Imo inda mu ke da gwamnan APC kuri'a 60,000 muka samu ko kusa da haka."

Ya cigaba da cewa:

''To ya kamata su karbi faduwa, su karbi kaddarar su, Allah ya na bada mulki ga wanda ya so. Abun da muke bukata shine a hada kai don cigaban kasar mu, na tabbatar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Peter Obi duk suna fatan alheri ga kasar nan, to su yarda sun fadi ko don cigaban kasarmu.''

Kara karanta wannan

“Mu Muka Ci Zaben Shugaban Kasa, Za Mu Kwato Hakkinmu” – Inji Datti Baba-Ahmed

Ahmada Lawan, Mutanen mazabata sun yi yanka da azumi don tazarce na

A wani labarin mun kawo muku cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce mutanen mazabarsa sun yanka dabobi irinsu rakuma da shanu tare da yin azumi don ganin ya samu nasara a zaben sanata na Arewacin Yobe.

Lawan ya ce ya zama dole ya jinjinawa al'ummar na yankinsa saboda bai taba ganin irin wannan kauna da soyayya da suka nuna masa ba, The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel