Tirƙashi: Wani Ɗan Acaɓa Ya Samu Nasarar Zama Ɗan Majalisa Kaduna

Tirƙashi: Wani Ɗan Acaɓa Ya Samu Nasarar Zama Ɗan Majalisa Kaduna

  • Mutumin Mai Suna Mathew ya taɓa Zama Kansila, Halin Rayuwa Yasa Ya Koma Sana'ar Kabu-Kabu wato Acaɓa.
  • Ɗan Achaɓan Yayi Wa Jam'iyyar APC, PDP, NNPP Fintinkau Da Ƙuri'u 10,508 Wacce Tabashi Nasara.
  • Ɗan Takarar daya Sha Kayi, Ya Amshi Ƙaddara Sannan Yayi Godiya Ga Yan Dangwalen da Suka Bashi Dama Tunda Fari.

Haƙiƙa Allah ne ke bada mulki ga wanda yaso kuma ya ƙwace mulkin daya bayar a lokacin da yaso.

Wani abin al'ajabi ya faru a Jihar Kaduna wanda ya daɗe yana bawa mutane mamaki gamida ɗaure kai.

Hakan ya samo asali ne sakamakon yadda wani ɗan acaba a jihar ta Kaduna daya zama ɗan majalisa a ƙarƙashin jam'iyyar Labor party wacce Peter Obi yakewa takarar shugaban ƙasa.

Mathew
Donatus Mathew: Dan Achaba CIke da Murna Zaije Majalisa Hoto: Leadership.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: APC Tayi Kaca-Kaca Da PDP a Jihar Kwara, Ta Lashe Kujerun Sanatocin Jihar

Mutumin mai suna Mr Donatus Mathew, tuni baturen zaɓe ya sanar da lashe zaɓen da yayi na gundumar Kaura dake jihar Kaduna.

Da baturen zaɓen yake sanar da lashe zaɓen na ɗan Acaɓar, Farfesa Elijah Ella yace Mathew ya samu adadin ƙuriu guda 10,508 cicif.

Wanda hakan ya bashi dama domin hamɓarar da mai wakiltar Kauran a majalisar tarayya a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP wato Gideon Lucas Gwani wanda yazo na biyu da adadin ƙuriu 10, 297.

Rahotanni dai sun nuna cewa, Mathew ya taɓa zama kansila a yankinsa, amma yanayin yau da gobe da matsin rayuwa yasa ya kama sana'ar achaɓa.

Mutane sunsha ganin Mathew yana jigilar kai fasinjoji wuraren da zasu je. Amma yau ya zama ɗan majalisa mai jiran rantsar wa.

Rahotanni Leadership sun nuna cewa Mr. Mathew mutum ne mai gaskiya da riƙon amana kuma ɗan ƙasa nagari.

Kwamishinan zaɓen ya ƙara jaddada cewa, ɗan takarar da jam'iyyar APC ta tsayar ya samu ƙuriu 9,919, yayin da ɗan takarar jam'iyyar NNPP ya samu ƙuria guda 5,354, wanda hakan na nuna APC tazo ta uku, NNPP kuma tazo ta huɗu.

Kara karanta wannan

A Kwantar Da Hankali, Kada a Kaiwa Igbo Hari, Inji Tinubu akan Rashin Nasararsa a Legos

Mr Donatus Mathew, ɗan takarar daya sha kayi, ya zanta da manema labarai jim kaɗan da sanar da zaɓen, inda ya godewa waɗanda suka zaɓe sa ya wakilce su a majalisar wakilai ta ƙasa, yace, yarda dashi da sukayi ya wakilce abune mai saka shi alfahari har kullum.

Wani labarin kuma, Kabiru Gaya yasha kashi a Hannun Kawu Sumailaa Kano. Ko yaya hakan ta Faru?

Sanatan APC Kabiru Gaya Yasha Ƙasa a Hannun Ɗan Takarar NNPP Kawu Sumaila.

Ɗan takarar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, Kawu Sumaila, ya lallasa abokin hamayyar sa na jam'iyyar APC Sanata Kabiru Gaya wanda ya daɗe yana wakiltar yankinsa a Kano ta Kudu.

Kawu Sumaila yana kan gaba a mafi yawan ƙananan hukumomin da aka kammala bayyana sakamakon su Sanata.

Kabiru Gaya na jam'iyyar APC, ya shafe tsawon lokaci yana wakilci a majalisar dattawan Najeriya.

Yanzu ta tabbata, bazai koma ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel