Zaɓen 2023: Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Sanatocin Jihar Kwara

Zaɓen 2023: Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Sanatocin Jihar Kwara

  • Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe dukkanin kujerun sanatacin jihar Kwara
  • Ƴan takarar na jam'iyyar ta APC sun samu wannan gagarumar nasarar ne bayan sun doke abokan takarar su na sauran jam'iyyun
  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) itace ta sanar da sakamakon zaɓen a hukumance

Jihar Kwara- Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da ƴan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin waɗanda suka lashe kujerun sanatocin jihar Kwara.

Sanata Oyelola Ashiru, an bayyana shi matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Kwara ta Kudu.

Sanata Ashiru ya samu nasara inda zai koma majalisar dattawa a karo na biyu. Rahoton The Nation.

Jam'iyyar APC
Zaɓen 2023: Jam'iyyar APC Ta Lashe Kujerun Sanatocin Jihar Kwara Hoto: The Nation
Asali: UGC

Farfesa Ajibola Akanbi, shine ya sanar da hakan a cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta Omu Aran.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Shiri Ya Kwana: PDP Tayi Biji-Biji Da APC a Ƙaramar Hukumar El-Rufai

Farfesa Akanbi ya ce Ashiru ya samu ƙuri'u 55,966 yayin da sanata Rafiu Ibrahim na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu ƙuri'u 34,950.

Farfesa Wale Suleiman na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ya zo na uku inda ya samu ƙuri'u 2,4215.

Haka kuma a kujerar sanatan Kwara ta Arewa, an bayyana Alhaji Umar Sadiq, a matsayin wanda ya lashe zaɓen. 

Sadiq ya samu ƙuri'u 78,015 inda ya doke mai biye da shi a zaɓen, Issa Bawa Adamu na jam'iyyar PDP, wanda ya samu ƙuri'u 41,443, yayin da ƴar takakar jam'iyyar LP, Moses Rebecca ta samu ƙuri'u 1,947.

Haka nan kuma ɗan takarar kujerar sanatan Kwara ta Tsakiya a jam'iyyar APC, Mallam Saliu Mustapha, ya samu nasara a zaɓen sa. Rahoton Thisday

Saliu Mustapha ya samu ƙuri'u 109,823 inda ya doke ɗan takarar jam'iyyar PDP, Bolaji Abdullahi, wanda ya samu ƙuri'u 69,202.

Yayin da ɗan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Ridwan Apaokagi ya samu ƙuri'u 13,193, Akanbi Farook na Labour Party (LP) ya samu ƙuri'u9,280.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Shan Kashi a Legas, Tinubu Ya Farfaɗo a Wata Jihar Arewacin Najeriya

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, na shugaban ƙasa, Peter Obi, ya samu ruwan ƙuri'u a jihar Enugu.

Ɗan takarar ya lashe dukkanin ƙananan hukumomin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel