Bola Tinubu ya Magantu Kan Rade-Rafin Kara Aure da Ake Yadawa Zai yi

Bola Tinubu ya Magantu Kan Rade-Rafin Kara Aure da Ake Yadawa Zai yi

  • Asiwaju Bola Tinubu ya karyata batun kara aurensa da ya karade ko ina a yanar gizo, inda ya bayyana yadda suke zaune lami lafiya gami da more rayuwar aurensu shi da matarsa
  • 'Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, ya kara da cewa, shi bai da niyyar dankaro wa matarsa kishiya, batu ne kawai na masu son janyo rikici cikin iyalinsa
  • Ya kara da cewa, burinsu ba zai taba cika ba, saboda shi da matarsa a yanzu sun fi mayar da hankali kan fafutukar yakin neman kuri'un don lashe zaben shugaban kasa

'Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya karyata "Wani labarin kanzon kurege" da ke yawo a yanar gizo cewa zai kara aure, inda ya bayyana yadda yake jindadin rayuwar aurensa da matarsa, Sanata Oluremi..

Kara karanta wannan

Karya Ne, Babu Wanda Ya Yiwa Mai Mala Buni Rajamu: Ahmad Lawan

Remi Tinubu
Bola Tinubu ya Magantu Kan Rade-Rafin Kara Aure da Ake Yadawa Zai yi. Hoto daga Vanguardngr.news
Asali: UGC

Mai magana da yawunsa, Tundra Rahman ne ya bayyana hakan a wata takarda mai taken,:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ku Daina Yada Labarin Kanzon Kurege: Asiwaju Bola Tinubu bai da niyyar kara aure.”

Takarda wacce ta fita daren Lahadi a Abuja.

"Mun ga labaran kanzon kuregen da ke yawo a yanar gizo na cewa 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu zai kara aure.
"Wannan labarin kanzon kurege ne wanda bai da tushe.
"Shi Asiwaju na morar aurensa da matarsa, Sanata Oluremi Tinubu, wacce aka albarkata da 'ya'ya na kwarai. Bai shirya kara aure ba, Musulma ko Kirista.”

- Kamar yadda takardar ta bayyana daga Ofishin yada labaran Tinubu.

Kamar yadda takardar ta bayyana:

”Burin wadan da ke yada cewa zai auri musulma ba kawai don su janyo rikici cikin iyalin Tinubu kadai bane, sai don su jawo kiyayya tsakanin al'ummar kiristanci.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa: Duk Dan Takarar Da Wike Ya Marawa Baya Ba Zai Ci Zabe Ba, Malamin Addini Ya Yi Gargadi

"Burinsu ba zai cika ba. Hakan ba zai yi tasiri ba."

Takardar ta roki 'yan Najeriya da su yi watsi da labarin karyar.

"A halin yanzu, Asiwaju ya maida hankalinsa kan kamfen don lashe zaben shugaban kasa da zai gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, ko ya dawo wa jama'a buri, data da tsaro da farincikin Najeriya.
"Sanata Oluremi ita ma tana tsaka da fafutukar nemar wa mijinta magoya baya. Hankalinsu bazai dawo ga abaran kanzon kurege ba,"

- Kamar yadda takardar ta kara.

Karancin tsabar kudi: Hadimin Buhari ya fallasa yadda yake kashe N20, 000 a mako

A wani labari na daban, Femi Adesina ya koka kan karancin tsabar kudi da ya addabi kasar nan.

Hadimin shugaban kasan yace ya kwashe mako daya yana kashe N20,000 saboda rashin tsabar kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel