Femi Adesina, Hadimin Buhari Ya Bayyana Yadda Yake Kashe N20,000 a Sati Daya

Femi Adesina, Hadimin Buhari Ya Bayyana Yadda Yake Kashe N20,000 a Sati Daya

  • Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina, ya koka kan rashin tsabar kudi inda yace N20,000 yayi mako daya yana kashewa
  • Ya sanar da yadda ya kira ma'aikacin banki amma aka ce masa iyakar abinda zai samu kenan, kuma ya hakura ya karba yana maneji
  • Yace jin dadinsa da abinci a gidansa, da babu kuwa tsaf zai hada Garrin kwaki da gyadarsa ya dinga cika cikinsa da su

Mai bada shawara na musamman ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa wannan rashin tsabar kudin ya dame shi duba da sauyin fasalin takardun Naira da babban bankin Najeriya tayi.

Femi Adesina
Gowon, Jonathan da Obasanjo Sun Halarci Taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya. Hoto daga punch.ng
Asali: UGC

Adesina a wata takarda da ya fitar yace, mako daya yayi yana kashe N20,000.

Hadimin shugaban kasan yayi bayanin yadda ya ke rayuwa kan hakan duk da rashin tsabar kudi da ya addabi kasar.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Aiki Ya Kwabe Maku, Ku Je Ku Koyi Dambe, Shehu Sani Ga Ma'aikatan Banki

Adesina yace, shi tare da wasu sun kama hanya za su je Bauchi, Legas, Senegal, Katsina, Kano da Jigawa daga ranar 23 na Janairu zuwa 31 na Janairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Bana son zama kamar nakasasshe mara wayau, wanda aka cewa ga yaki na zuwa amma ya tsaya a inda yake. Na tattara koma, duk wani kudi na kuma na aika da shi banki. Bana son kudin halal di na su zama abinda zasu kare a gidan tarihi."
"Babban bankin Najeriya daga baya ya samu damar kara kwanaki 10 daga Shugaba kasa Muhammadu Buhari, wanda yanzu kotu koli ta tsawaita. Amma bai canza ba da cewa yanzu a sati N20,000 nake kashewa kuma ina cigaba da kashewa."

Adesina yace ya kashe N6,000 na tsawon kwanaki uku kuma zuwa Juma'a, zai kankance zuwa N2,500.

Kara karanta wannan

2023: Ina Fatan a yi Zabukan Najeriya, Kada Dalilin Dagawa yazo, Olusegun Obasanjo

Yace da yawan 'yan Najeriya basu san cewa jami'an gwamnati suna fama ba inda ya goyi bayan kalamansa da:

"Ana ruwa, kasa na shanyewa."

Ya kara da bayyana cewa, ya kira ma'aikacin bankin inda yake masa korafi kan hakan amma yayi masa dariya.

"Bayan ganin cewa da gaske nake, yace abinda kawai zai iya yi shi ne samo maka N20,000 ta ATM, wanda shi ne abinda za a iya ba kowa a rana. Toh, da babu gara babu dadi.
"Na aika direbana ya karbar min kudin kuma na kashe dukkan abubuwan da zan yi na bi layi. Idan ka zauna a gida, kana kallon kwallo da farin ciki, ba za ka bukaci kashe kudi sosai ba."

- Yace.

Mai bada shawarar na musamman, yace kalubalen farko da ya fuskanta shi ne cika tankin motarsa wanda zai kwashe masa N15,000.

Ya yanke shawarar siyan mai na N8,000 daga Juma'a zuwa Laraba. Kuma abun jin dadin shi ne akwai abinci a gida, idan kuma da babu, zai sha Garri da gyada.

Kara karanta wannan

Saraki Ya Magantu Kan Zaben Shugaban Kasa Na 2023: Ya Fada Ma Yan Najeriya Abun da Za Su Yi Wa APC

Atiku ya yi alkawarin farfado da kasuwanci a Yobe

A wani labari na daban, Atiku Abubakar, 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya sha alwashin farfado da kasuwanci ta hanyar bude iyakoki.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace zai tabbatar da zaman lafiya ya dawo jihar da ke arewa maso gabas din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel