Duk Wanda Wike Ya Marawa Baya Cikin Yan Takarar Shugaban Kasa Ba Zai Kai Labari ba – Primate Ayodele Ga Tinubu

Duk Wanda Wike Ya Marawa Baya Cikin Yan Takarar Shugaban Kasa Ba Zai Kai Labari ba – Primate Ayodele Ga Tinubu

  • Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa duk dan takarar shugaban kasa da Gwamna Nyesom Wike ya marawa baya ba zai kai labari ba a zabe mai zuwa
  • Limamin coci, Ayodele ya bayyana cewa Wike zai addasa annoba ga takarar shugabancin Asiwaju Bola Tinubu
  • Ayodele ya bayyana cewa gwamnan na Ribas na wasa da damar da yake da shi a siyasa da wadannan abubuwa da ya ke aikatawa a baya-bayan nan

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana cewa rade-radin da ake yi na cewa Gwamna Nyesom Wike na goyon bayan dn takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ba zai cimma nasara ba.

A wata sanarwa da kakakinsa, Osho Oluwatosin, ya saki, Primate Ayodele ya bayyana cewa Gwamna Wike zai dai kawo tangarda ne kawai ga kudirin shugabancin Tinubu, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwanan Wike Ya Marawa Tinubu Baya? Tsohon Hadimin Buhari Ya Fadi Gaskiya

Primate Ayodele, Bola Tinubu da Nyesom Wike
Tinubu: Duk Wanda Wike Ya Marawa Baya Cikin Yan Takarar Shugaban Kasa Ba Zai Kai Labari ba – Primate Ayodele Hoto: @GovWike, @tsg2023
Asali: Twitter

Wike na wasa da makomar siyasarsa, Primate Ayodele

Malamin addinin ya yi bayanin cewa gwamnan na jihar Ribas yana wasa ne da makomar siyasarsa ne da matakan da ya dauka a baya-bayan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta nakalto Ayodele yana cewa:

"APC da Tinubu za su sha kaye a jihar Ribas. Goyon bayan Tinubu da Wike ke yi annoba ce, duk wanda gwamnan ya marawa ba baya zai sha kaye ko shakka babu.
"Wike na wasa ne da makomar siyasarsa kuma wannan zai masa illa sosai. Mutanensa ba za su saurare shi ba saboda ya wuce iyakarsa."

Za a yi wa Peter Obi taron dangi a arewa, Primate Ayodele

A gefe guda, mun ji a baya cewa Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen abun da zai wakana kwanaki 13 kafin babban zaben Najeriya wanda za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

‘Danuwan Tsohon Gwamna Ya Fadawa Duniya Wanda Wike Yake Goyon Baya a Boye

Ayodele ya bayyana cewa akwai wasu tawaga da za su yi wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi taron dangi a arewa don kada ya kai labari a babban zaben kasar mai zuwa.

Sai dai ya yi kira ga Obi da ya hankalta sosai, inda ya ce ba za a yi juyin mulki ba a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel